Akwai Yiwuwar Gwamna Makinde Ba Zai Halarci Taron Gangamin Atiku Ba a Jiharsa

Akwai Yiwuwar Gwamna Makinde Ba Zai Halarci Taron Gangamin Atiku Ba a Jiharsa

  • Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP zai yi gangamin kamfen a jihar Oyo, amma ana kyautata zaton ba zai samu halartar gwamnan jihar ba
  • Wannan na zuwa ne yayin da aka ga an kammala shirye-shirye ba tare da hannun gwamna Seyi Makinde na Oyo ba
  • Ana ci gaba da zaman doya da manja tsakanin dan takarar shugaban kasa na PDP da wasu gwamnoni biyar da ake kira G-5

Najeriya - Alamu sun nuna cewa, gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde ba zai halarci taron kamfen jam’iyyar PDP da za a gudanar a jiharsa na dan takarar shugaban kasa Atiku Abubakar ba a yau.

Leadership ta tattaro cewa, ‘yan takarar majalisar tarayya a jihar sun shiga rudanin ko dai su halarci taron gangamin ko sabanin haka.

Ana kyautata zaton gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke ne zai jagoranci ‘yan takarar gwamna a jihohin Ogun da Legas zuwa wannan babban taron.

Kara karanta wannan

Wike Ya Samu Tangarɗa, Gwamnan G-5 Ya Yi Magana Mai Jan Hankali Kan Yuwuwar Haɗewa da Atiku

Gwamna Makinde ba zai halarci kamfen Atiku ba
Akwai Yiwuwar Gwamna Makinde Ba Zai Halarci Taron Gangamin Atiku Ba a Jiharsa | Hoto: Dailypost.ng
Asali: UGC

Daga baya an fahimci cewa, Makinde bai samu sahhalewar tawagar gwamnonin G-5 masu adawa da Atiku ba don halartar taron na jihar tasa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yadda gwamnonin G-5 suka ziyarci jihar Oyo a baya

Ba kamar yadda gwamnonin G-5 suka ziyarci Ibadan a kwanakin baya ba, ya zuwa yanzu dai babu wani abu da ke maraba da Atiku da shugabannin PDP a garin.

Hakazalika, an ce wurin taron; Mapo Hall da sauran abubuwa daga shirin taron bai zo daga gwamna Makinde na jihar ba.

Idan baku manta ba, tsohon gwamna Ayodele Fayose da masu mara masa baya, musamman ‘yan takarar sanata da majalisar wakilai basu halarci taron gangamin PDP na jihar Ekiti ba, rahoton TheCable.

Gwamnonin G-5 masu adawa da shugabancin PDP da Atiku

Makinde da sauran gwamnoni hudu da suka hada da na Ribas, Benue, Abia da Enugu ba sa cikin tawagar kamfen dan takarar shugaban kasa Atiku duk da cewa su ma mambobin PDP ne.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Daya Daga Cikin Gwamnonin G-5 Ya Sauya Tunani, Zai Hade da Atiku Abubakar

Wannan ya faru ne sakamakon adawa da suke da shugabancin jam’iyyar PDP a matakin kasa, suna neman a gaggauta tsige Ayu Iyorchia a matsayin shugaban PDP na kasa.

A baya gwamna Wike ya bayyana irin dan takarar da tawagar G-5 za ta zaba, kuma ya ce nan ba dadewa ba zai bayyana wanda yake so.

Asali: Legit.ng

Online view pixel