2023: Kwankwaso Ya Zolayi Obi A Chatham House, Ya Ce Jamiyyar Labour Tamkar Gishirin 'Andrews Liver Salt' Ne
- Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso, a ranar Laraba ya tafi Chatham House da ke Birtaniya don magana kan takararsa
- Yayin da ya ke magana kan shirinsa ga yan Najeriya da sauran siyasar kasar a yan kwanan nan, Kwankwaso ya zolayi jam'iyyar Labour da dan takararta Peter Obi
- Da ya ke magana kan dalilin da yasa ya ki yin maja da LP, Kwankwaso ya ce jam'iyyar Labour kamar gishirin 'Andrews Liver Salt' ne da ke tashi nan take kuma ta fadi
UK - Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso, a ranar Laraba, 18 ga watan Janairu, ya zolayi jam'iyyar Labour, LP.
A Chatham House, yayin da ya ke magana kan dalilin da yasa bai yi maja da jam'iyyar Labour ta Peter Obi ba, ya ce tamkar gishirin 'Andrews Liver Salt' ta ke, za ta tashi amma nan take zai ta fadi, Channels TV ta rahoto.

Kara karanta wannan
Kwankwaso Ya Tono Asalin Matsala, Ya Fadi Abu Ɗaya Tak Da Ya Kawo Yan Bindiga Arewacin Najeirya

Asali: Facebook
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Kwankwaso ya zolayi jam'iyyar Labour
Yayin da ya ke zolayar Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na LP, Kwankwaso ya ce:
"Jam'iyyar mu ce kadai jam'iyyar da ta girma a Najeriya a yau ... a wurin mu (Jam'iyyar Labour), kamar gishirin "Andrews Liver Salt" ne, ta zo (nan take) ta fara yin zama yanzu kuma tana sauka kasa. Wannan shine gaskiya, a lura da haka."
Kwankwaso ya bayyana hakan ne a yayin da ya ke jawabi a Chatham House da ke Landan, inda ya yi magana kan maudu'i 'Nigeria’s 2023 elections: Service delivery and policy alternatives'.
Yan Najeriya sun yi martani
Yan Najeriya a Twitter sun ta bayyana ra'ayoyinsu kan jawabin na Kwankwaso.
@vonasc ya rubuta:
"Peter Obi bai kira sunan kowa ba ko wata jam'iyya a jawabinsa na Chatham House ... Kwankwaso yana son tallata kansa ta hanyar kashewa jam'iyyar Labour kasuwa kuma duniya na gani."

Kara karanta wannan
Kwankwaso Ya Yi Maganar Janye Takara, Ya Fadi Abin da Zai Sa Ya Hakura da Neman Mulki
@I_vomitSense ya ce:
"Saboda karamin tambaya fa, kana tsangwamar wata kabila da dan takara da yanki.
"Basira na da amfani."
@Mr_CHIDI_PETERS ya rubuta:
"Mun ji ka... Muna son ganin yadda abin zai kaya.
"Ta taimake mu karasa yin Ubangiji a arewa... Ko mai ka ce mana, muna son ka.."
@iamshurubab cewa ya yi:
"Rikici"
@Uzo_wmh ya rubuta:
"Wannan jawabi ta yi armashi, cigaba da gashi."
Asali: Legit.ng