An Kori Shugabannin Makarantun Sakandare 12 Domin Karɓar 'Kuɗin Haramun' Daga Ɗalibai

An Kori Shugabannin Makarantun Sakandare 12 Domin Karɓar 'Kuɗin Haramun' Daga Ɗalibai

  • Gwamnatin jihar Cross Rivers ta sallami malamai wasu shugabannin makarantun sakandari 12 kan 'rashawa'
  • Kwamishinan ilimi na jihar Cross Rivers, Godwin Amanke ne ya bayyana hakan a ranar Talata lokacin da ya ke jawabi ga manema labarai
  • Amanke ya kuma ce an dakatar da wasu shugabannin makarantu shida sannan an canja wa wasu 16 wuraren aiki

Cross Rivers - Gwamnatin Cross Rivers ta sallami shugabannin makarantun sakandare 12 kan zarginsu da karbar kudi ba bisa ka'ida ba daga dalibai a jihar.

Godwin Amanke, kwamishinan ingantaccen ilimi a jihar ne ya bayyana hakan yayin jawabi da manema labarai a Calabar, ranar Talata, rahoton The Cable.

Makaranta
An Kori Shugabannin Makarantun Sakandare 12 Domin Karɓar 'Kuɗin Haramun' Daga Ɗalibai. Hoto: The Cable.
Asali: Facebook

An kori malamai 12, an dakatar da shida an canja wa 16 wurin aiki a Cross Rivers, Amande

Amanke ya ce an dakatar da wasu shida saboda laifuka masu kama da wannan yayin da wasu 16 aka sauya musu wurin aiki.

Kara karanta wannan

Karin bayani: Jirgin ministan wata kasa ya fado a kan makarantar yara, mutum 16 sun mutu

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce:

"Mun bada takardun amsa korafi da dama. An cire shugabannin makarantu guda 12, an dakatar da shida an kuma yi wa 16 canjin wurin aiki."

Kwamishinan ya ce wasu da abin ya shafa sun biya shugabannin makarantun N300,000 don a musu canji zuwa wasu makarantu.

Ya kuma ce gwamnati na kokarin farfado da darajar ilimi a jihar.

Amanke ya ce gwamnatin jihar ta tura jami'anta makarantun sakandare a jihar don magance matsalar kungiyoyin asiri, rahoton The Punch.

Wannan cigaban na zuwa ne a yayin da hukumar ilimin firamari na jihar, (SUBEB) ta sanar cewa ta kammala shirin horas da malaman firamari 12,000 a jihar.

Stephen Odey, shugaban hukumar SUBEB na jihar, ya ce horaswar za ta tabbatar malaman sun kware kan dabarun zamani na koyarwa.

A cewarsa:

"Za a bada horaswar don ganin malamai wadata a kowanne lungu da sako na jihar.

Kara karanta wannan

Kwamandoji Abu Ubaidah da Malam Yusuf Tare da Mayaka 40 na Boko Haram Sun Sheka Lahira Bayan Luguden NAF

"Manyan kwararrun masu bada horaswa da masana ilimi ne za su yi horaswa."

Rashin albashi na wata shida ya saka malaman firamare zanga-zanga a Cross Rivers

A wani rahoton, wasu malaman makarantun firamare a Cross Rivers wadanda aka rage wa mukami a 2016, sun yi zanga-zanga a Calabar kan kin biyansu albashi na wata shida.

Wasu cikin malaman da suka yi magana da yan jarida a Calabar sun ce hukumar SUBEB ce ta dakatar da albashinsu sannan wasu cikinsu ma sun riga mu gidan gaskiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel