Yan Bindiga Sun Saki Manoma 2 Da Suka Sace A Hanyarsu Ta Dawowa Daga Gona Bayan Biyan Naira Miliyan 6

Yan Bindiga Sun Saki Manoma 2 Da Suka Sace A Hanyarsu Ta Dawowa Daga Gona Bayan Biyan Naira Miliyan 6

  • Mr Samuel Oyedotun da Mr Tobiloba Fashola, manoma guda biyu da masu garkuwa da mutane suka sace a jihar Osun sun tsira
  • Tun dai a ranar Laraba na makon da ya gabata ne masu garkuwan suka sace manoman biyu suka nemi naira miliyan 25 a matsayin kudin fansa
  • Daga bisani sun rage zuwa naira miliyan 6 amma suka tsare yan uwan wadanda aka yi garkuwar yayin da suka kai kudin fansar, daga bisani sun sake su baki daya

Jihar Osun - Masu garkuwa da mutane da suka sace manoma biyu a Osun, Samuel Oyedotun da Tobiloba Fashola sun sake su tare da wanda ya tafi biyan kudin fansa.

The Nation ta rahoto cewa an sace manoman biyu ne yayin da suke hanyar dawowa daga gonarsu da ke Ede/Ileoogbo road a karamar hukumar Ayedire na jihar Osun a ranar Laraba da ta gabata, kuma masu garkuwan suka nemi a biya naira miliyan 25.

Kara karanta wannan

Doka a hannu: Kiristoci a jihar Arewa sun fusata, sun kone ofishin 'yan sanda saboda abu 1

Taswirar Jihar Osun
Yan Bindiga Sun Saki Manoma 2 Da Suka Sace A Hanyarsu Ta Dawowa Daga Gona Bayan Biyan Naira Miliyan 6. Hoto: @VanguardNG
Asali: Twitter

Daga bisani masu garkuwan sun yarda sun karbi naira miliyan 6 sannan aka kai musu a wani gari da ke kan iyakar jihar Kogi da Kwara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An tsare yan uwansu uku da suka tafi kai kudin fansar ciki har da yayan Samuel mai suna Sunday bayan sun karbi kudin, suka sake neman a sake biyan wani naira miliyan 24.

Dangin manoman da aka sace ya tabbatar da cewa an sako su

Rahotanni sun ce wani majiya na kusa da iyalan, a ranar Laraba ya tabbatar da cewa Samuel da Tobiloba da aka fara sacewa da farko sun shaki iskar yanci.

Hakazalika, wani danginsu da shima yana daga cikin wadanda suka tafi kai kudin fansar shima a sake shi a jihar Kogi.

Da aka tuntube shi kan sakinsu, mai magana da yawun yan sandan jihar Osun, Yemisi Opalola ya tabbatar da afkuwar lamarin.

Kara karanta wannan

Allahu Akbar: Yadda Malami da Matarsa Suka Mutu a Kokarin Ceto Dansu Daga Nutsewa a Ruwa

Jami'an tsaro sun kama wasu yan fashin daji da ake zargin masu garkuwa da mutane ne

Kun ji cewa jami'an yan sanda a jihar Edo sun kama wasu yan bindiga mutane biyar da ake zargi masu garkuwa da mutane don karbar fansa ne.

Daga cikin wadanda aka kama akwai Matthew Osayande dan shekara 32; Bankole Faz dan shekara 35; Christopher Aiyegbeni dan shekara 29; Uyi Destiny dan shekara 27 da Ayemen Okojie dan shekara 32.

Asali: Legit.ng

Online view pixel