Ka Zo Ka Karba ‘Dan ka: Dattijuwa ga Gwamnan Legas, Sanwo Olu

Ka Zo Ka Karba ‘Dan ka: Dattijuwa ga Gwamnan Legas, Sanwo Olu

  • Wata mata mai shekaru 47, Grace Moses ta maka gwamnan jihar Legas kotu, inda tayi kira ga gwamna Babajide Sanwo-Olu da yazo ya amsa 'dansa
  • A cewar matar, baya da taimakon Ubangiji da yanzu 'danta ya dade da halakata, yanzu tunda ya girma yazo ya amsa abunsa
  • Haka zalika, ta bayyana yadda suka yi soyayya da gwamnan a 1995 a Delta, inda ya dirka mata ciki ya barta da jigila har zuwa yanzu bai waiwayeta da 'dan da ta haifa ba

Delta - Wata mata mai shekaru 47, Grace Moses, ta bayyana gaban wata babbar kotu a jihar Delta, ranar Talata, inda tayi kira ga gwamnan jihar Legas, Mr Babajide Sanwo-Olu, da yazo ya amsa 'dansa.

Sanwo Olu
Ka Zo Ka Karba ‘Dan ka: Dattijuwa ga Gwamnan Legas, Sanwo Olu. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Yayin zantawa da manema labarai jim kadan bayan kotu ta dage sauraron karar da ke da alaka da gwamnan da 'danta, Emmanuel, matar ta ce,:

Kara karanta wannan

Da Duminsa: 'Yan Bindiga Sun Kai Farmakin Ba-zata Yankunan Sokoto, Sun yi Awon Gaba da Dabbobi

"Sakon da zan aika ga Sanwo-Olu shi ne, yazo ya karbi 'dansa. Yanzu yaron ya girma. Yana bani ciwon kai. Bacin taimakon Ubangiji, da yanzu na dade da mutuwa.
"Saboda cikin da ka dirkamin, na daina zuwa makaranta domin wutar da mahaifiyata ta huramin gami da fattakata daga gidan saboda sun jira Sanwo-Olu amma hakan bai yuwu ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Yayin da nayi yunkurin zubar da cikin, nasha "Tsami, amma ya ki zubewa.
"Na koma siyar da alale ga mutane, suna biya na N150 wanda nayi amfani dashi don ni da jinjirina mu rayu. Yanzu jinjirin ya girma yana barazanar halaka ni idan ban nuna masa mahaifinsa ba."

Yadda muka hadu da Gwamnan Legas, Dattijuwa

Matar ta bayyana yadda ta hadu da gwmanan jihar Legas din a 1995 lokacin yana da shekaru 19.

"A lokacin, gwamna Sanwo-Olu na aiki a wani kamfanin man fetur, Saipem a anguwar Ubogo cikin karamar hukumar Udu da ke jihar Delta.

Kara karanta wannan

Ba zan taba fashi ba: Shigan da malamar aji ta yi ya girgiza dalibai, jama'a sun yi martani

"Mun fara soyayya wanda yayi sanadin juna biyu. Gwamnan ya kai ni asibiti cikin anguwar Agbarho, arewacin karamar hukumar Ughellu inda aka zubda cikin."

Matar wacce ke turancin titi ta ce:

"Bayan wasu kwanaki, Sanwo-Olu ya kara kwanciya da ni wanda yayi sanadin wani juna biyun."
"Tun daga nan, Sanwo-Olu yayi watsi dani ya bar jihar da ikirarin an masa canjin wurin aiki zuwa Maiduguri, jihar Borno.
"Ya barni da ragamar juna biyun da jinjirin da na haifa ba tare da taimakon wani daga cikin danginsa ba.
"Na fadawa 'dana, Emmanuel Sanwo-Olu cewa mahaifinsa ba musaki bane. Har zuwa yanzu, ya ki saurarena da 'dansa Emmanuel.”

Daily Trust ta rahoto cewa, yayin zantawa da manema labarai, Emanuel ya ce Sanwo-Olu bai taba waiwayensa ba, inda ya kara da cewa, duk iya kokarin ganin ya gana dashi bai yiwu ba.

A cewar Emmanuel:

"Ni ba ina bin mahaifina bane don yana da kudi ko yanzu shine gwamnan Legas. Kawai ina so in san shi ne mahaifina.

Kara karanta wannan

2023: Gwamna Wike Ya Gindaya Wa Atiku, PDP Sharadi Na Karshe Gabanin Ranar Zabe

"Mahaifiyata ta shida min yadda ta hadu da mahaifina, Babajide Sanwo-Olu shekaru da dama da suka shude...,
"Babu wani daga cikin 'yan uwan mahaifina da nake gani. Abun yana damuna saboda abokaina na mun dariya."

Sai dai, kotu ta dage karar zuwa 13 ga watan Fabrairu, 2023 don cigaba da sauraro.

Mr. john Aikpokpo-Martins, lauyan Emmanuel da mahaifiyarsa, ya ce Sanwo-Olu ya shigar da kalubalantar karar cewa yana da shamaki game da lamarin a matsayinsa na gwamna.

Asali: Legit.ng

Online view pixel