Firgici da Tashin Hankali Yayin da 'Yan Bindiga Suka Kutsa Yankunan Sokoto

Firgici da Tashin Hankali Yayin da 'Yan Bindiga Suka Kutsa Yankunan Sokoto

  • Firgici da fargaba ya darsu a zukatan mazauna yankuna biyu, Bubari da Durbawa duk a Denge-Shuni na kananan hukumomin kudancin jihar Sakkwato
  • Hakan ya biyo bayan wasu da ake zargi 'yan bindiga ne suka yi dirar mikiya a anguwannin kan babura a yammacin Lahadi gami da budewa mazauna yankin wuta
  • Sai dai, wata majiya ta shaidawa manema labarai yadda harin bai ritsa da kowa ba, amma barayin sun yi awon gaba da wasu dabbobin kauyen

Sokoto - An shiga firgici da damuwa a yammacin Lahadi yayin da wasu da ake zargi 'yan bindiga ne suka kutsa yankuna biyu na Sakkwato.

Taswirar Sokoto
Firgici da Tashin Hankali Yayin da 'Yan Bindiga Suka Kutsa Yankunan Sokoto. Hoto daga thenationonlineng.net
Asali: UGC

Yankuna biyun, kamar yadda wata majiya da ta zanta da wakilin Punch Metro ta bayyana su ne Bubari da Durbawa, duk a Denge-Shuni da Sakkwato da ke kananan hukumomin jihar.

Kara karanta wannan

Dakarun Sojin Najeriya Sun Sheke Shugaban 'Yan Bindiga, Kachalla Gudau, Har Lahira a Katsina

Wata majiya da ta zanta da wakilin Punch Metro ta waya ta bayyana yadda 'yan bindiga su ka yi dirar mikiya a Durbawa da Bubari kan babura gami da budewa jama'an anguwar wuta.

Sai dai, majiyar ba ta iya tabbatar da ko hakan ya ritsa da wani ba, amma ta bayyana yadda wadanda ake zargin su ka yi awon gaba da wasu daga cikin dabbobin kauyen.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sai dai, rundunar 'yan sandan jihar Sakkwato ta tabbatar da harin, inda ta bada tabbacin yadda jami'an tsaro ke kan bincikar lamarin.

Kakakin rundunar, DSP Sanusi Abubakar, a wani sakon waya da yayi martani ga wakilin Punch Metro inda ya ce,

"muna kan binciken lamarin,"

Miyagun sun kutsa cocin Katsina, Sun sace masu bauta 25

A wani labari na daban, wasu 'yan ta'adda da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun kai hari har cikin wata majami'a da ke Jan Tsauni a yankin karamar hukumar Kankara ta jihar Katsina.

Kara karanta wannan

Matasa Sun Halaka Basarake a Jihar Arewa, Gwamna Ya Kakaba Dokar Zaman Gida

An gano yadda suka jigata babban faston cocin inda suka bar shi a wahale tare da yin awon gaba da masu bauta har su ashirin da biyar.

Lamarin ya faru ne a ranar Lahadi 15 ga watan Janairun 2023 wurin karfe 10 na safe yayin da masu bauta suka tsunduma cikin ibada.

Tuni dai jami'an tsaro suka bazama ceto wadanda aka sacen.

Asali: Legit.ng

Online view pixel