Kun Tafka Abun Kunya: Bidiyon Fasto Yana Fada ga Mabiyansa Kan Sadakar N100 da Suka bayar

Kun Tafka Abun Kunya: Bidiyon Fasto Yana Fada ga Mabiyansa Kan Sadakar N100 da Suka bayar

  • Wani fusataccen faston Najeriya ya huce fushinsa tare da nuna rashin jin dadinsa a cocinsa da irin kudin da mambobin ke bayarwa na sadaka
  • A bidiyon da yanzu yake ta yawo a soshiyal midiya, ya caccaki masu bayar da sadakar N100 da N20 inda yace abun kunya ne bada sadakar irin wannan kudin
  • Martani daban-daban sun cika bidiyon inda aka dinga caccakar faston tare da sukar yadda ya nuna son kudinsa karara babu ko boyewa

Wani bidiyon faston Najeriya yana sukar mambobin cocinsa kan sadakar N100 da N20 da suka zuba masa ya tada kura a soshiyal midiya.

Faston da har yanzu ba a gano sunansa ba ya dinga magana da yaren ibo inda ya nuna bacin ransa kan irin kankantar kudin tare da cewa ko man fetur lita 20 suka siya na cocin kullum.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Kare ya Firgita Bayan Yayi Ido 4 da Zaki, Ya Haidye Haushi da ya Fara don Tsoro

Fusataccen Fasto
Kun Tafka Abun Kunya: Bidiyon Fasto Yana Fada ga Mabiyansa Kan Sadakar N100 da Suka bayar. Hoto daga TikTok/@oracleofmoney2023
Asali: UGC

Tare da mikar da hannu cike da fusata ta gaban mambobin cocin, ya bayyana cewa babban abun kunya ne ga duk wanda ya zuba masa wannan kudin matsayin sadaka.

Cikakken abinda faston yace a bidiyon TikTok din shi ne:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Siyan fetur mu ke yi lita 20 a kowanne lokacin bauta. Kun ji kunya da ku ke ba wa Ubangiji N100. Ku da ku ka zo wannan cocin, kun ji kunya.
"Wasu za su zo cocin daga waje su samu albrakar, amma ku da ku ke zaune a mazauni ba za ku samu komai ba.
"Babu yadda za a yi Ubangiji ya bukaci in siya masa fetur amma in tashi cike da alfahari daga mazauni na in bayar da N100.
"Ko wadanda ke ba Ubangiji N20, yaro ne yana bara."

Kara karanta wannan

Yadda ‘Yan ‘Yahoo Suka Damfari Tsohuwa, Suka Sace Duka Dukiyar da ta Mallaka

Soshiyal midiya tayi martani

Pretty Oma tace:

"Idan kowa ya saka N100, ta yaya fasto zai siya man fetur a wannan tsadar man da ake yi."

mbonujoyce tace:

"Ta yaya za ka je coci da N100. Ba fa dole idan ba ka da shi, amma idan da anko ne tuni za ku je ku samo kudi."

Prince Kenny yace:

"Me yasa ku ke fusata wannan faston? Ku dinga kokartawa mana kuna saka kudi. Toh me ma na sani? Amma kuma babu abinda yayi yawa ko kadan a sadaka."

Emirate ID yace:

"Ku kalla fasto fa. Wannan mutumin bai san halin da kasar nan ta saka jama'a ba."

Diamond Paints IND LTD yace:

"Fasto abin da fa mutum ya ke da shi, shi zai ba Ubangiji. Kada ka fusata."

Bidiyon matashi mai kama da Buhari ya je siyan man fetur

A wani labari na daban, wani matashi mai matukar kama da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bar jama'a baki bude.

A bidiyon da ya bayyana, an ga matashin yayi shiga tsaf irin ta shugaban kasan kuma ya harde hannayensa a baya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel