Budurwa Yar Abuja Da ke Karban Albashi Rabin Miliyan Na Neman Miji, Ta Fadi Sharuddanta

Budurwa Yar Abuja Da ke Karban Albashi Rabin Miliyan Na Neman Miji, Ta Fadi Sharuddanta

  • Wata matashiyar lauya mai shekaru 29 tana neman mijin aure kuma ta bayyana sharuddan da take so wanda zai nemi aurenta ya cika
  • Matashiyar budurwar mazauniyar Abuja wacce ke karbar albashi rabin miliyan duk wata ta bayyana cewa tana jin yaruka uku
  • Budurwar na son namiji wanda ke da aiki mai kyau, salihi kuma wanda ya fi ta tsawo

Abuja - Wata matashiyar budurwa mazauniyar Abuja ta kaddamar da bukatarta na neman mijin aure wanda ya dace da ra'ayinta.

Dandalin kulla aure na Musulunci mai suna @Halal_Match ya wallafa irin mijin da budurwar ta ke nema yayin da ta gindaya sharudda ga mazan da ke ra'ayinta a Twitter.

Budurwa
Budurwa Yar Abuja Da ke Karban Albashi Rabin Miliyan Na Neman Miji, Ta Fadi Sharuddanta Hoto: MoMo Productions
Asali: Getty Images

@Halal_Match ya bayyana cewa matashiyar da ke karban albashi rabin miliyan duk wata ta kasance siririyar lauya bakar faa wacce tsawonta ya kai 5'6, tana kuma jin yaruka uku sannan tana saka gilashin ido.

Kara karanta wannan

Ba Zan Yi Lefe Ba: Matashi Na Neman Karin Mata Ta Biyu, Ya Ce Zai Biya Sadakin Miliyan N1 da Wasu Sharudda

Matashiyar wacce ta fito daga jahar Adamawa tana son namiji Musulmi wanda ke da aiki mai kyau a Abuja da hankali.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dandalin ya kuma kara da cewar tana son namijin da ya fi ta tsawo kuma zai ta so wanda ke jin yaruka da yawa.

Budurwar ta kara da cewar a shirye take ta fita shakatawa a karshen makon nan, tana mai nuna shirinta na son barin layin yan mata nan kusa.

Ana sa ran duk wanda ke ra'ayinta zai tuntube ta ta adireshin imel da aka saka a jikin wallafar.

Kalli wallafarta a kasa:

Jama'a sun yi martani

@Pharieydah_M ta ce:

"Lmao ta yaya saka albashinta ya zama matsala? Wani ma ya ce hakan na nuna tana da izza, amma idan da namiji ne ba za a yi masa kallon haka ba fa. Yar'uwa dan Allah lissafa abuj da kike so watakila ki samu."

Kara karanta wannan

Ko da ne ga dan siyasa: Bidiyon mahaukaciyar da ta haifi jariri a kasuwa ya bar baya da kura

@manga9tee ta ce:

"Duk ba wannan ba, kin iya karatun Qur'ani da kyau? Wani irin sani kika yiwa addinin Islama? Kina saka hijabi ko kina cikin mata masu yawo tsirara da sunan wayewa? Wannan shine tambayoyin da ya kamata duk wani mai tunani ko ra'ayi ya tambaya."

@mudson6 ya ce:

"Yar'uwa ki sassauto mana, bai dace ki fadi nauyin aljihunki baa dandalin neman aure. Zai janyo hankalin maza gareki wadanda za ki zo ki yi danasani.
"Na yi tsammanin adimin za ta shawarce ki."

Kyakkyawar budurwa ta bar saurayinta mai kudi, ta auri mai nakasu

A wani labarin, mun ji cewa wata kyakkyawar budurwa ta rabu da hadadden saurayinta mai kudi don auren miji mai nakasu.

Budurwar mai suna Poly ta ce a ranar da ta fara ganin mijin nata nan take son shi ya kama ta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel