Peter Obi Zai Kai Ziyara Arewa, Zai Gana da Shugabannin Addinai da Sarakuna a Jihar Kaduna

Peter Obi Zai Kai Ziyara Arewa, Zai Gana da Shugabannin Addinai da Sarakuna a Jihar Kaduna

  • Jihar Kaduna za ta yi babban bako, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour zai kus-kus da malaman addini
  • Hakazalika, rahoto ya ce Peter Obi zai zauna da Sarkin Zazzau da na Jema'a duk dai a jihar ta Kaduna da ke Arewa maso Yamma
  • Peter Obi na ci gaba da fadada takararsa da neman goyon bayan manyan mutane a yankin Arewacin Najeriya da Kudancinta

Jihar Kaduna - Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar Labour, Peter Obi zai yi zaman tattaunawa da shugabannin addinai a yankin Kaduna ta Kudu, kana zai ziyarci sarakuna a yankin.

Hakazalika, Obi zai gudanar da wani taron gangami a filin wasa na Ahmadu Bello da ke Kaduna, inda zai gana da dalibai daga makatrantu daban-daban da kuma ‘yan a mutun jam’iyyar da magoya bayansa.

Kara karanta wannan

Atiku Ya Tona Asirin Manyan Yan Takara Biyu, Yace Hatsari Ne Babba a Zabe Su a 2023

Wannan na fitowa ne daga bakin kakakin jam’iyyar, Dr Yunusa Tanko a yayin wata gwarya-gwaryar zama a jihar Kaduna, Daily Trust ta ruwaito.

Peter Obi zai zauna da sarakuna biyu a Arewa
Peter Obi Zai Kai Ziyara Arewa, Zai Gana da Shugabannin Addinai da Sarakuna a Jihar Kaduna | Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Obi zai gana da Sarkin Zazzau da na Jema'a

Ya kuma bayyana cewa, Obi zai kai ziyara zuwa fadar Sarkin Zazzau, Amb, Ahmad Nuhu Bamalli da kuma Sarkin Jema’a a Kafancan da ke yankin Kudancin jihar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Dr Tanko ya kuma bayyana cewa, a yayin taron na kamfen, Obi zai karanto manufofinsa bakwai da yake son cimmawa idan aka zabe shi a matsayin shugaban kasa a zaben bana.

Peter Obi na ci gaba da tallata kansa da manufofinsa ga ‘yan Najeriya, hakazalika, yakan fadi maganganu da nuna nagarta da kwarewarsa a mulki.

Obi ya sha bayyanawa ‘yan Najeriya cewa, shi ya cancanci ya gaji Buhari a zaben bana, lamarin da ke kara daukar hankali a kasar.

Kara karanta wannan

2023: Bidiyon Yadda Aka Ceci Fitaccen Dan Takarar Shugaban Kasa Daga Tulin Jama'a Ya Fito

A tun farko, ya dauko abokin takararsa daga Arewacin Najeriya kuma dan jihar Kaduna, Dr Datti Baba-Ahmed.

Asali: Legit.ng

Online view pixel