Gwamnati Za Ta Fara Duba Albashin da Kowane Ma’aikaci yake Karba a Jihohi 36
- NSIWC ta ce a watan nan za a aika da Jami’ai domin sa ido a kan tsarin mafi karancin albashi
- Kakakin Hukumar, Emmanuel Njoku ya bada wannan sanarwa da ya zanta da manema labarai
- Njoku ya ce jami’an NSIWC za su duba ko ma’aikatu su na bin dokar mafi karancin albashi na 2019
Abua - Hukumar NSIWC da ke da alhakin tsara albashi da samun ma’aikata a Najeriya, ya fara yin zama domin duba mafi karancin albashi.
Vanguard ta rahoto shugaban sashen kula da jama’a na NSIWC, Emmanuel Njoku ya yi wannan bayani a wani jawabi da ya fitar a yammacin Lahadi.
A jawabin Mista Emmanuel Njoku, an fahimci sai a shekarar 2024 za a kammala wannan aiki.
NSIWC tayi zama dabam-dabam tare da bada horaswa na musamman a fadin kasar nan domin duba dokar mafi karan albashi na shekarar 2019.
A makon gobe aiki zai kankama
A ranar 23 ga watan Junairun nan za a fara aikin duba albashin gadan-gadan domin ganin yadda hukumomi da kamfanoni suke bin sabuwar dokar.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Ma’aikatan NSIWC za kuma suyi bincike domin gano ko ma’aikatu su na da bayanin albashin da suke biya da sauran romon da jami’ansu ke samu.
Rahoton yake cewa aikin zai wayar da kan masu aiki a cibiyoyo, ma’aikatu da hukumomin gwamnati da kamfanin ‘yan kasuwa a kan hakkinsu.
Daga wannan aiki ne hukumar NSIWC za ta iya samun alkaluman albashin da ake biyan wadanda suke aiki a kamfanoni, bayanan da aka rasa a yau.
Za a ratsa ko ina a Najeriya
NSIWC za ta tura tawaga zuwa babban birnin tarayya na Abuja da jihohohi 36 da ake da su a Najeriya, jaridar The Cable ta rahoto Njoku yana fadan haka.
Kakakin ya sanar da ma’aikatun gwamatin tarayya, jihohi, kananan hukumomi, kamfanonin ‘yan kasuwa da ‘yan kwadago su bada hadin-kai sosai.
Za a zakulo wadanda za suyi aikin ne daga ma’aikatun kwadago, tattalin arziki, sannan daga ofisoshin shugaban ma’aikata, Akanta Janar da NBS.
Baya ga babban birnin tarayya na Abuja, NSIWC za ta tura tawaga zuwa jihohohi 36 da ake da su.
Makasudin shi ne ganin ko ma’aikata su na karbar akalla N30, 000 a matsayin albashin wata kamar yadda Muhammadu Buhari ya sa hannu a 2019.
Babu karin albashi - FG
A kwanaki baya aka samu labari Gwamnatin Muhammadu Buhari ta bayyana cewa babu ma’aikacin da za ayi wa karin albashi a sabuwar shekarar nan.
Chris Ngige ya fitar da wata sanarwa ta musamman ta bakin mai magana da yawun ma’aikatar kwadago, Olajide Oshundun yana karin haske kan batun.
Asali: Legit.ng