Mai Juna Biyu Ta Gamu da Mijinta Yana Sharholiya da Budurwa, An Yi Dirama Bidiyo

Mai Juna Biyu Ta Gamu da Mijinta Yana Sharholiya da Budurwa, An Yi Dirama Bidiyo

  • Wata mai juna biyu ta labarta yadda mijinta ya karya mata zuciya bayan ta gano yana cin amanarta a waje
  • A wani bidiyo da aka wallafa a Soshiyal Midiya, matar ta bayyana cewa abokin rayuwarta ya mata karyan zai je ganin kakarsa
  • Awanni bayan ya tafi ne ta samu labarin ya kammala shirye-shiryen tafiya sharholiya da wata abokiyar aikinsa mace

Wata matar aure ta bayyana mijinta da makaryaci kuma wanda ke cin amanarta tare da wata abokiyar aikinsa.

A wani bidiyo da ke yawo a soshiyal Midiya, matar ta tona asirin mijin wanda ya mata karya cewa zai tafi sada zumunci ne wurin Kakarsa.

Cin amana a zaman aure.
Mai Juna Biyu Ta Gamu da Mijinta Yana Sharholiya da Budurwa, An Yi Dirama Bidiyo
Asali: Getty Images

Sai dai tana zaune ta samu kira daga kawarta, wacce ta gaya mata cewa to ga mijinta nan ya gama shirinsa zai tafi sharholiya da wata da suke aiki a wuri ɗaya.

Kara karanta wannan

Yan Najeriya Sun Zagaye Mai Kama Da Shugaba Buhari a Wani Bidiyo Da Ya Yadu

Bayan samun wannan tsegumi, matar ta kira mijin ba daya b, ba biyu amma sai ya rika katse kiran, ya ki ɗaga ko daya daga ciki.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Nan take ta shirya ta nufi filin jirgin sama, da zuwa ta hange shi tare da budurwar sanye da rigar da ya siya mata irinta. Zuciyarta ta raya mata zuwa ta tunkare su.

Yayin da take ba da labarin yadda abun ya faru a TikTok, matar wacce zuciyarta ta sosu ta bayyana cewa tana dauke da juna biyun ɗansu na farko.

Kalli bidiyon a nan

Martanin jama'a a soshiyal midiya

@wayndette014 yace:

"Kar ki je wurin su, jaririn dake cikinki ne abun damuwa a yanzu da kuma lafiyarki. Ki dan yi kuka sannan ki nemi wurin da zaki samu nutsuwa, daga nan ki nemi rabuwa da shi."

Kara karanta wannan

Ina Biyan Kudin Haya N800k Duk Shekara: Budurwa Ta Nuna Cikin Dakinta Da ke Da Wuta 24/7

@veronicam013 yace:

"Haba ki barta ta samu abinda ba ta da shi, kama gabanki kawai ki gaba. Ki gode wa mai sama kin gano halinsa tun yanzu ba sai bayan shekara 23 ba."

@shawnkelly81 ya ce:

"Kar ki tunkare su, ki tausayawa kanki da abinda ke cikinki, ki bari ya ganki sai ki tafi gida, ki watsar da kayansa waje ki sauya makullan gida."

A wani labarin kuma Kwana Hudu da Aure, Amarya Ta Kama Angonta da Yar Uwarta Suna Jin Dadi a Gado

Wata mata ta ja hankalin ma'abota shafukan sada zumunta bayan ta tona yadda ta kama Mijinta na holewarsa a gado tare da 'yar uwarta kwanaki huɗu da ɗaura musu aure.

Asali: Legit.ng

Online view pixel