Kotu Koli ta Tsige Rawanin Babban Basarake a Yankin Kudancin Najeriya

Kotu Koli ta Tsige Rawanin Babban Basarake a Yankin Kudancin Najeriya

  • Kotun koli ta Najeriya, ta tube rawanin babban basarake Edidem Ekpo Okon Abasi Otu V wanda shi ne Obong na masarautar Calabar
  • An gano cewa, an dinga tafka shari’ar tun shekarar 2008 wacce tayi daidai da shekaru 15 bayan nada sarkin kuma ga hate karagar mulkin
  • An gano cewa, ba ya cikin wadanda aka zaba a karon farko kafin a fara tantance wadanda aka zaba domin hawa karagar mulkin

Calabar - Kotun koli ta tuge Edidem Ekpo Okon Abasi Otu V, mai sarautar Obong na Calabar, jaridar Daily Trust ta rahoto.

A hukuncin da Jastis Mohammed Lawal Garba, kotun ta umarci masu nada sarakuna da majalisar sarakunan gargajiya da su hanzarta fara bin tsarin samar da wani Obong na Calabar.

Da Dumi
Kotu Koli ta Tsige Rawanin Babban Basarake a Yankin Kudancin Najeriya
Asali: Original

Kotun ta yanke hukuncin cewa a yi zaben sabon sarkin dogaro da kundin tsarin fadar na 2002.

Kara karanta wannan

Hotunan Buhari, Mamman Daura, Gwamnoni, Jiga-Jigai SUn Halarci Daurin Auren Diyar Abba Kyari

Tsohon Ministan kudin karkashin mulkin Janar Sani Abacha, Etubom Anthony Ani da wasu a kara mai lamba HC/102/2008 wacce shugaban lauyoyinsu Joe Agi, SAN ya shigar, Otu da sauran a matsayinsu na mambobin majalisar sarakunan gargajiya na kudancin Calabar da yin magudi a tsarin tantance sabon sarkin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kotun tayi umarnin cewa:

“Wanda ake kara na farko Etubum Ani wanda ya amsa cewa ba ya cikin wadanda aka fara zabe domin tantancewa yayin zaben sabon sakin kuma hakan yasa bashi da damar samun kuri’a ko daya.
“Mai daukaka kara na farko Abasi Otu a gargajiyance ya cancanta samun kuri’u.”

Don hakan kotun daukaka kara da soke tsarin da aka bi aka samar da Etubum Ani matsayin ‘dan takarar.

An nada Ambasada Bamallo sabon sarkin Zazzau

A wani labari na daban, Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya nada Ambasada Ahmad Nuhu Bamalli sabon sarkin Zazzau.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Kotun koli ta yanke hukuncin karshe kan karar Mohammad Sani Abacha

Hakan ya biyo bayan mutuwar tsohon basarake, Alhaji Shehu Idris wanda yayi sama da shekaru 40 kan karagar mulkin Zazzau.

Sarautar Zazzau ta koma gidan Mallawa bayan kusan shekaru 100 da ta bar gidan tun bayan rasuwar Malam Musa.

Bashir Aminu ya je Kotu

Tsohon Iyan Zazzau, Alhaji Bashir Aminu ya maka gwamnatin jihar Kaduna a kotu kan nadin sarautar wacce ya ce sabon sarkin Zazzau ne bai cancanta ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel