Kotun Koli Ta Yanke Hukuncin Karshe Kan Karar Mohammad Sani Abacha

Kotun Koli Ta Yanke Hukuncin Karshe Kan Karar Mohammad Sani Abacha

  • Yunkurin iyalan gidan marigayi Janar Sani Abacha na kokarin dakatad da binciken kudaden da ake zargin mahaifinsu ya wawura lokacin mulkinsa ya sake gamo da tangarda
  • Kotun kolin Najeriya ta yi watsi da karar da babban 'dansa Mohammed Abacha ya shigar na hana gwamnati sake bude takardar bincike
  • Alkali Emmanuel Agim na kotun kolin Najeriya ya ce karar bata da wani gaskiya cikinta

Abuja - Gwamnatin tarayya ta samu nasara a kotun Allah ya isa kan iyalan marigayi tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Janar Sani Abacha,, bisa zargin da ake musu na hannu cikin wawuran kudin kasa da mahaifinsu yayi.

Gwamnati na son kwato wasu makudan miliyoyi da ake zargin marigayin ya boye a wasu kasashe irinsu Amurka da Bailiwick of Jersey.

Kotun koli a ranar Juma'a, 13 ga Junairu, ta yi watsi da daukaka karar da iyalan marigayi Abacha suka shigar inda suka bukaci kotun ta hana gwamnati bude takardun bincike kan mahaifinsu da wasu iyalansa da ake zargi da hannu.

Kara karanta wannan

Gaskiya daya ce: Fitaccen Sarki a Arewa ya ba 'yan siyasa shawari game da zaben gwamnoni

Marigayi Abacha
Kotun Koli Ta Yanke Hukuncin Karshe Kan Karar Mohammad Sani Abacha Hoto: Archives

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Hukuncin kotu

Alkalan kotun kili karkashin jagorancin Alkali Emmanuel Agim, sun yi ittifakin cewa bincike ya nuna gaskiya cikin bukatar da iyalan Abacha sukayi.

Saboda haka ya yi watsi da karar kuma hakan ya bawa gwamnatin daman cigaba da tuhumarsu, rahoton The Nigerian Tribune.

PDP A Kano: Aminu Wali Ya Bayyana Matakin Da Zai Dauka Bayan Kotu Ta Ba Wa Abacha Nasara

A wani labarin kuwa, Korarren dan takarar gwamna na PDP a jihar Kano, Sadiq Aminu Wali, ya bayyana niyarsa na zuwa kotun daukaka kara bayan babban kotun tarayya ta soke zabensa da aka yi a matsayin dan takarar gwamna a jihar.

Daily Trust ta rahoto cewa Babban Kotun Tarayya da ke Kano ta ayyana Mohammed Sani Abacha a matsayin halastaccen dan takarar gwamna na PDP a Kano.

Kara karanta wannan

2023: Abokin Takarar Atiku Ya Fasa Kwai, Ya Faɗi Manyan Dalilin da Yasa Peter Obi Ya Samu Nasara a Shiyyoyi 2

A yayin yanke hukuncin, Mai shari'a A.M. Liman ya umurci hukumar zabe mai zaman kanta, INEC, ta sauya sunan Wali da na Abacha.

Daga nan kotun ta amince da zaben fidda gwani na bangaren Shehu Sagagi da aka gudanar a Lugard House, wacce ta samar da Abacha a matsayin dan takarar gwamna a maimakon na bangaren Wali da aka gudanar a cibiyar matasa na Sani Abacha.

Asali: Legit.ng

Online view pixel