Dakarun Sojojin Najeriya Sun Murkushe Yan Ta'adda Sama da 100 a Yankin Arewa

Dakarun Sojojin Najeriya Sun Murkushe Yan Ta'adda Sama da 100 a Yankin Arewa

  • Dakarun sojojin Najriya na ci gaba da samun nasara a yaki da suke da yan ta’adda a kasar
  • Sojoji sun murkushe yan Boko Haram da mayakan ISWAP fiye da 50 a cikin makonni uku da suka gabata
  • Dakarun sun kuma kama yan ta’adda 37, masu kai masu kaya 21, masu kai kwarmato biyu yan kasar waje da masu garkuwa da mutane biyar

Hedkwatar tsaro ta ce dakarun rundunar sojoji sun murkushe yan ta’adda fiye da 50 a ayyuka daban-daban da suka gudanar a yankunan arewa maso gabas da arewa maso yamma cikin makonni uku.

Daraktan labarai na ayyukan tsaro, Manjo Janar Musa Danmadami wanda ya yi jawabi ga manema labarai ya ce dakarun Operation Hadin Kai sun murkushe yan Boko haram da ISWAP 23 tsakanin 25 ga watan Disamba da 12 ga watan Janairu a arewa maso gabas.

Kara karanta wannan

Hawaye Sun Kwaranya Yayin da Yan Bindiga Suka Halaka Amarya da Ango Yan Kwanaki Kafin Aurensu

Manjo Janar Danmadami
Dakarun Sojojin Najeriya Sun Murkushe Yan Ta'adda Sama da 100 a Yankin Arewa Hoto: @DefenceInfoNG
Asali: Twitter

Dakarun sun kuma kama yan ta’adda 18 da masu kai masu kayayyaki 21 da wasu masu kai kwarmato yan kasar waje su biyu da kuma masu garkuwa da mutane biyar a fadin yankin, rahoton The Nation.

Danmadami ya kuma bayyana cewa dakarun sun kuma ceto yan farin hula 47 yayin da yan ta’adda 377 da iyalansu da suka hada da maza 52, mata 126 da yara 199 suka mika wuya ga sojoji.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce an mika kayayyakin da aka kwato, yan ta’addan da aka kama da yan farar hular da aka ceto ga hukumar da ya dace don daukar mataki na gaba.

Wani bangare na jawabinsa na cewa:

“An mika yan ta’addan da aka kama da wadanda suka mika wuya tare da iyalinsu inda ya dace don mataki na gaba. Cikin makonni uku da suka gabata, dakarun soji sun kwato bindigogin AK47 guda 21, bindigogin FN hudu, bindigogin gargajiya uku, kananan bindigogin guda biyar da bindigar toka uku.”

Kara karanta wannan

Kwararan Dalilai 5 Dake Nuna Cewa Wajibi CBN Ya Dage Ranar Daina Amfani da Tsaffin Takardun Naira

A arewa maso yamma, Danmadami ya ce dakarun Operation Hadarin Daji sun kai zazzafar hari mabuyar yan ta’adda da sansanoninsu a yankin.

Ya ce dakarun sun kashe yan ta’adda 25, sun kama 19 sannan suka ceto yan farar hula 68, yayin da sojojin sama suka kuma tayar da wasu miyagun.

Kakakin tsaron ya kara da cewar dakarun sun kuma kama wani mai hada kai da yan ta’adda a Madachi, karamar hukumar Dandume da ke jihar Katsina da damin kudi naira miliyan 1.5 rahoton Punch.

A cewarsa, wani mai suna Nasiru, kasurgumin dan ta’adda da jami’an tsaro ke nema ruwa a jallo ne ya aika wanda ake zargin.

Ya ce:

“Nasiru ne ke da alhakin kashe mutane da dama a karamar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna."

An kama matasa uku kan sace yarinya yar shekara 6

A wani labari na daban, rundunar yan sandan jihar Katsina ta yi ram da wasu matasa uku bayan sun yi garkuwa da wata yarinya yar shekaru 6.

Matasan sun sace Fatima Abubakar a jihar Kano sannan suka tafi da ita Katsina inda suka nemi a biya kudin fansarta naira miliyan biyu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel