Dalilai 5 Dake Nuna Cewa CBN Zai Dage Ranar Daina Amfani da Tsaffin Takardun Naira

Dalilai 5 Dake Nuna Cewa CBN Zai Dage Ranar Daina Amfani da Tsaffin Takardun Naira

Kawo yau Lahadi, 29 ga watan Junairu, 2023, saura kwanaki 2 daidai da karewar wa'adin da gwamnatin tarayya ta baiwa yan Najeriya su mayar da tsaffin takardun Nairansu banki.

Babban bankin Najeriya CBN ya bayyana cewa yana kan bakansa ba zai dage ranar karshe ta 31 ga Junairu , 2023 da ya sanya ba.

CBN ya jaddada hakan duk da kiraye-kirayen da yan Najeriya, yan majalisa, kungiyoyi da masana ke yiwa gwamnan bankin, Godwin Emefiele.

Amma akwai wasu alamu dake nuna cewa zai zama wajibi a dage ranar.

Sabbin
Dalilai 6 Dake Nuna Cewa CBN Zai Dage Ranar Daina Amfani da Tsaffin Takardun Naira
Asali: Getty Images

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Legit ta tattaro muku wadannan dalilai 7:

1. Har yanzu ana samun tsaffin kudi a ATM

Duk da ana saura kwanaki 2 da karewar wa'adin, har yanzu ana samun tsaffin kudade na fitowa daga bakinna'urorin ATM ba bankuna.

Kara karanta wannan

Saura ranar aiki 1 kacal, CBN Tace Ta Fitar Da Sabbin Kudi N120m Jihar Katsina

Mai sharhi kan manyan labarun jarida na tashar AriseTV, Emmanuel Efeni, yace ko kwanan ya cire kudi daga ATM kuma tsaffi ne.

Duk da umurnin da CBN ya yiwa bankuna a farkon makon nan, da alamun da sauran rina a kaba.

2. Shugabanin bankuna sun ce ko su basu da issasun sabbin kudi.

A ranar Alhamis, shugabannin bankuna a Najeriya sun zanna da kwamitin majalisar wkailan tarayya.

Shugabannin bankuna sun yi ittifakin cewa lallai akwai bukatar dage ranar 31 ga Junairu da aka sanya.

Daya daga cikin shugabannin bankunan, Hadiza Ambursa wacce ta wakilci Access Bank ta bayyana cewa abinda ya kamata shine suna karban kudi su zuba cikin na'urorin ATM.

Amma su kansu basu samun isassun kudin.

Hakazalika Shehu Aliyu daga First Bank ya ce ra'ayin yan majalisa na a dage ranar shine maganar gaskiya.

3. Yan Najeriya da dama ko ganin sabbin kudin basu yi ba

Kara karanta wannan

Canjin Takardun Kudi: Kira Zuwa Ga Hukuma, Daga Dr Sani Rijiyar Lemo

An fitar da sabbin kudaden ranar 15 ga Disamba, 2022, amma bayan kimanin wata gida yanzu, akwai daruruwan yan Najeriyan da ko taba kudin basu yi ba.

Wasu yan Najeriya a karkara da birane sun ce ko ganin yadda kudaden suke basu yi ba.

Aisha Sadiq, yar makaranta mazauniyar Abuja ta bayyana cewa ita har yanzu bata yi ido biyu da sabbin kudin ba.

Usman Ahmed shi kuma ya laburta mana cewa shi Naira 1000 kadai ya gani.

4. Kiraye-kirayen masu fada aji ga gwamnati ta dage ranar

Mai Alfarma sarkin Musulmi, Alhaji Atiku Abubakar, Sanata Rabiu Kwankwaso, Dr Sani Umar Rijijar Lemo, da sauran manyan masu fada a ji a Najeriya sun yi kira da shugaban kasa lallai ya dage wa'adin.

5. Gwamnoni sun sanya baki

Gwamnonin Najeriya ta zanna da gwamnan babban bankin Najeriya ta yanar gizo kuma bayyana masa akwai matsaloli game da lamarin haramta amfani da tsaffin takardun Naira.

Kara karanta wannan

Muna goyon bayan kira ga dage ranar daina amfani da tsaffin kudi, Shugabannin bankuna a Najeriya

Gwamnonin sun bayyana wa Godwin Emefiele cewa ya tausayawa talakawa da mutan karkara kafin daina amfani da tsohon kudi da kuma takaita adadin kuri'un za'a iya cirewa daga banki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel