Jami'an Tsaro Nigeria Sun Kashe Yan Bindiga 50 Tare Da Kama Wasu 62

Jami'an Tsaro Nigeria Sun Kashe Yan Bindiga 50 Tare Da Kama Wasu 62

  • Jami'an tsaron Nigeria na kirga riba wajen yaki da tsageru da yan ta'adda a Nigeria sakamakon kara kaimi da sukai
  • Rundunar tsaron Nigeria dake da shelikwata a Abuja ta sanar da nasarar da ta samu a kwananan a yakin da take da masu kawo cikas din zaman lafiya a Nigeria
  • Bayan Nasarorin da ta kirga harda kwace makamai masu tarin yawa da suka hada da bindigogi da kuma harsashai

Abuja - Shelikwatar rundunar taro ta sanar da kashe yan bindiga 50 tare da kama kusan 62, hadi da kama wasu bindigogi maau tarin yawa, a yankin arewacin kasar nan. Kamar yadda jaridar Thisday ta rawaito.

Sannan rundunar tace ta tseratar da akalla wanda akai garkuwa da su kusan mutum 47, sannan yan Boko Haram da yan kungiyar ISWAP su 377 ne suka yi saranda a yayin hare-haren jami'an.

Kara karanta wannan

Rundunar Sojojin Najeriya Ta Kashe Yan Ta’adda Sama da 50 Cikin Makonni Uku, Inji Hedkwatar Tsaro

Darakatan kula da harkar sadarwa da aiyuka DDMO, Maj Gen Musa Danmadami ne ya bayyana hakan a loakcin da yake bayyana nasarorin rundunar na sati uku.

Sojoji
Jami'an Tsaro Nigeria SUn Kashe Yan Bindiga 50 Tare Da Kama Wasu 62 Hoto: Thisday
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yace wannan na cikin kudirin rundunar na yakar ta'addanci a Nigeria, kamar yadda yace.

"A kokarin da muke na ganin an samu zaman lafiya mai dorewa, sojojinmu da kuma sauran hukumomin tsaro sunyi namijin kokari wajen kashe yan ta'adda kusan 50 tare da kama wasu 62.
"Ba iya haka ba, sai da suka samu nasara kwato makamai da jharsashe daga wajen yan ta'addan wanda yawansu yakai 55"

Ya ci gaba da cewa akwai daga cikin yan ta'addan sun miki wuya, yana mai cewa:

"Daga cikin wanda suka mika wuya daga yan ta'addan akwai maza 52 da mata 126 da kuma kananan yara kusan 199"

A lokaxin da rundunar ke wannan kkokarin akwai wadanda akai garkuwa da su kusan mutum 43 da rundunar ta samu ta kubutar dasu, sannan kuma rundunar ta samu nasar samun kudade muraran a wajen yan ta'addan da yawansu yakai 50m

Kara karanta wannan

Kwararan Dalilai 5 Dake Nuna Cewa Wajibi CBN Ya Dage Ranar Daina Amfani da Tsaffin Takardun Naira

Karin Abubuwan Da Aka Samu

Jaridar Bussinesstoday tace ba iya abunda dakurun sojin suka samu ba kenan, akwai karin wasu makaman da rundunar ta kwato.

Daga ciki akwai bindiga kirar AK47 da wata bindiga mai ta'adin tsiya mai suna PKT da kuma wasu harsashe masu yawan gaske da wayoyin hannu da kuma baburan hawa.

Jaridar ta rawaito cewa dukka abubuwan da rundunar ta samu tace ta mika su ga hukumomin da suka dace

Asali: Legit.ng

Online view pixel