INEC ta Bayyana Adadin 'Yan Najeriya da Suka yi Rijistar Zaben 2023

INEC ta Bayyana Adadin 'Yan Najeriya da Suka yi Rijistar Zaben 2023

  • Hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya ta sanar da cewa, mutum sama da miliyan 93 ne suka yi rijistar zaben 2023 mai zuwa
  • Kamar yadda hukumar ta bayyana a hedkwatarta da ke Abuja, ta sanar da cewa maza ne da kaso mafi yawa na masu rijistar zaben
  • A cikin jihohin Najeriya kuma, jihar Legas ce ke kan gaba wurin yawan masu kada kuri'un inda jihar Kano ke biye da ita

FCT, Abuja - Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, INEC, tace ta yi wa masu kada kuri'a 93,469,008 rijista domin zaben 2023 mai gabatowa.

Hukumar Zabe
INEC ta Bayyana Adadin 'Yan Najeriya da Suka yi Rijistar Zaben 2023. Hoto daga thenationonlineng.net
Asali: UGC

Bayanin kan wadanda suka yi rijistar ya nuna maza ne suka kwashe 52.5% yayin da mata suka kwashi 47.5% na jimillar wadanda suka yi rijistar, jaridar The Nation ta rahoto.

Kara karanta wannan

Yanzu: Shugaban INEC ya shigawa da shugabannin jam'iyyu 18, ya fadi adadin masu kada kuri'a

Wannan na kunshe ne a jerin sunaye na karshe na wadanda suka yi rijista da hukumar zaben mai zaman kanta ta bai wa jam'iyyun siyasa a ranar Laraba a hedkwatarsu da ke Abuja.

Legas ce a kan gaba inda ta ke da mutum 7,060,195, sai Kano da ke biye da 5,921,370 na wadanda suka yi rijistar zaben.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kamar yadda yace, Legas ce a kan gaba da masu kada kuri’u 7,060,195, jihar Kano na biye da 5,921,370 sai Kaduna da ke da 4,335,208.

A kuwa bangaren rarrabuwa na mazan da suka yi rijistar zabe 49,054,162 yayin da mata suke da yawan 44,054,846.

Hakazalika, matasa masu shekaru 18 zuwa 34 su ne suka zama masu rinjaye a shekaru da mutum 37,060,399 wanda ke wakiltar kashi 39.66 na masu kada kuri’a.

Jaridar TheCable ta rahoto hakan, sai kuma a bangaren sana’ar masu kada kuri’u, dalibai ne suke kan gaba da 26,027,481.

Kara karanta wannan

Bayar Da Ilimi Mai Nagarta Shine Zai Kawo Karshen Boko Haram A Nigeria Inji Buhari

Babu gudu ba ja da baya kan zabe, FG kan batun soke zabe

A wani labari na daban, gwamnatin tarayya ta bayyana cewa babu gudu babu ka da baya kan batun yin zaben 2023.

Gwamnatin tarayya tace ta shirya kuma hukumomin tsaro sun shirya don haka batun dagewa ko fasa yin zaben bai taso ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel