Okupe Ya Yi Magana Bayan DSS Ta Yi Ram da Shi a Filin Jirgin Sama a Legas

Okupe Ya Yi Magana Bayan DSS Ta Yi Ram da Shi a Filin Jirgin Sama a Legas

  • Tsohon hadimin Goodluck Jonathan, Doyin Okupe, ya kubuta daga hannun jami'an hukumar yaki da almundahana EFCC
  • A dazu ne jami'an hukumar tsaro ta farin kaya suka kama Okupe a filin jirgin saman Murtala Muhammed dake Legas
  • Tsohon DG na kamfen Peter Obi ya ce jami'ai sun kama shi ne bisa kuskure kuma yanzu haka sun sake shi sun ba shi hakuri

Abuja - Tsohon Datakta Janar na kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa a inuwar Labour Party, Doyin Okupe, ya kubuta daga hannun jami'an tsaro.

Jami'an tsaron farin kaya watau DSS ne suka yi ram da Okupe da safiyar ranar Alhamis 12 ga watan Janairu, 2023 a Filin sauka da tashin jiragen sama Murtala Muhammed Airport da ke jihar Legas.

Doyin Okupe.
Okupe Ya Yi Magana Bayan DSS Ta Yi Ram da Shi a Filin Jirgin Sama a Legas Hoto: thenationonline
Asali: UGC

Mai magana da yawun hukumar DSS, Dakta Peter Afunanya, ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Yan Bindiga Sun Kashe Yan Bijilante 3 A Wata Jihar Najeriya

Mista Afunanya ya bayyana cewa sun damke Okupe ne bisa umarnin hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) kuma sun mika musu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

EFCC ta sako Okupe

Amma a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na dandalin sada zumunta watau Tuwita, Mista Okupe, ya tabbatar da cewa ya kubuta daga hannun dakarun hukumar EFCC.

A rubutun, tsohon hadimin tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan, ya ce:

"An damke ni tare da tsare ni a Filin jirgin MM (Murtala Mohammed Airport) da safiyar nan 12 ga watan Janairu, 2023 lokacin ina kokarin barin kasa zuwa Birtaniya domin duba lafiya."
"Wannan ta faru ne shekaru bayan babbar Kotun tarayya mai zama a birnin tarayya Abuja ta rike Fasfo ɗina."
"Ba da jimawan nan ba na bar Ofishin hukumar EFCC bayan an sake ni inda manyan jami'an hukumar a Legas da Abuja suka bani hakuri kan kuskuren da aka samu."

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari Ya Cigaba da Yin Rabon Mukamai, Ya Nada Sabon Shugaban FHFL

Jiga-Jigan PDP sun tsallake rijiya da baya

A wani labarin kuma Hankula Sun Tashi Yayin da Wasu Jiga-Jigan PDP 15 Suka Yi Mummunan Hatsari a Hanyar Zuwa Kamfe

An ce lamarin ya rutsada yan siyasan ne a hanyar zuwa wurin taron bude fagen yakin nema zaben dan takarar gwamnan jihar Filato a inuwar PDP.

Bayanai sun nuna cewa duk da mambobin PDP na cikin hayyacin su, a yanzu an kwantar da masu raunuka a Asibitoci mabanbanta da ke jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel