Jiga-Jigan Jam'iyyar PDP 15 Sun Yi Hadari a Hanyar Zuwa Wurin Kamfe a Filato

Jiga-Jigan Jam'iyyar PDP 15 Sun Yi Hadari a Hanyar Zuwa Wurin Kamfe a Filato

  • Wasu jiga-jigan jam'iyyar PDP sun tsallake rijiya da baya yayin da Motar da suke ciki ta yi hatsari a hanyar zuwa wurin kamfe
  • Bayanai sun nuna cewa mambobin PDP sun yi hadari ne kafin isa wurin taron bude kamfen dan takarar gwamnan jihar Filato
  • A wata sanarwa da dan takarar ya fitar yace mambobin na kwance a Asibitin koyarwa na jami'ar Jos suna karban magani

Plateau - Akalla mambobin jam'iyyar PDP 15 ne suka tsallake rijiya da baya yayin da motarsu ta yi hatsari a hanyar zuwa gangamin kamfen dan takarar gwamnan jihar Filato, Caleb Mutfwang.

Jaridar Leadership ta tattaro cewa Motar Bas da ta dauko jiga-jigan PDP hatsari ya rutsa da ita a hanyar zuwa karamar hukumar Shendam, jihar Filato.

Jam'iyyar PDP.
Jiga-Jigan Jam'iyyar PDP 15 Sun Yi Hadari a Hanyar Zuwa Wurin Kamfe a Filato Hoto: leadership.ng
Asali: UGC

Bayanai sun nuna cewa duk da mambobin PDP na cikin hayyacin su, a yanzu an kwantar da masu raunuka a Asibitoci mabanbanta da ke jihar dake arewa ta tsakiya.

Kara karanta wannan

Adamawa Ta Cika Ta Batse Yayin da Shugaba Buhari Ya isa Mahaifar Atiku Don Yakin Neman Zaben APC

A wata sanarwa da Mangna Yusuf Wamyil, ya fitar a madadin dan takarar gwamna a inuwar PDP, yace Motar ta yi hadari ne da misalin karfe 10:00 na safe.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwan tace Motar Bas Toyota Hiace dauke da mambobin PDP a Filato na kan hanyar zuwa Shendam domin halartar kamfe sa'ilin da hatsarin ya rutsa da ita kusa da Bisichi Junction ranar Talata.

Wani sashin sanarwan ya ce:

"Wasu daga ciki sun samu rauni kuma tuni aka hanzarta kai su Asibitin koyarwa na jami'ar jiha (JUTH) Jos, inda masu ba da agaji da ma'aikatan lafiya ke kula da su."

Yusuf Wamyil ya kara da cewa bisa sa'a babu wanda ya rasa rayuwarsa sakamakon hatsarin da ya faru.

The Nation ta rahoto shi yana cewa:

"Muna mika jinjina ga jami'an hukumar kiyaye hadurra (FRSC) da sauran wadan da suka taimaka wurin daukar mutanen da suka ji raunuka zuwa Asibiti, mun yaba da hidimtawa al'umma."

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: An Kama Wani Mai Hannu a Garkuwa Fasinjojin Jirgin Kasa a Najeriya, Ya Fara Bayani

"Haka nan muna kira ga magoya baya da masu fatan Alheri da su taimaka da Addu'a domin majinyatan su warke cikin sauri da kuma Addu'ar Allah ya tsare tawagar kamfe har a kammala."

Yan arewa sun dawo rakiyar APC - Jibrin

A wani labarin kuma An Tono Babban Abinda APC Ta Rasa a Arewa Wanda Zai Ja Wa Tinubu Shan Kaye a Zaben 2023

Mai magana da yawun kwamitim kamfen jam'iyyar NNPP mai kayan marmari yace APC mai mulki ta rasa sama da kaso 70 na masu kaunarta a arewacin Najeriya.

Abdulmumini Jibrin, tsohon dan majalisar wakilan tarayya ya sauya sheka daga APC ne bayan fara nuna yatsa tsakansa da mai girma gwamnan Kano mai ci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel