Matashi Ya Kera 'Motar Kara' Harda Injin, Ya Tuka Abunsa a Bidiyo

Matashi Ya Kera 'Motar Kara' Harda Injin, Ya Tuka Abunsa a Bidiyo

  • Wani matashiya ya faso gari da 'motar kara' da ya kera sannan ya saka wani injin da ya yi kama da mashin
  • Cike da sha'awa, mutane da dama sun taru don ganin yadda mashin din ke aiki lokacin da mutumin ya tuka ta a taron jama'a
  • Yayin da wasu suka jinjinawa fasaharsa, wasu sun bata rai bayan cin karo da bidiyon

Masu amfani da Instagram sun yi martani a kan bidiyon wani mutumi da ya kera 'motar kara' sannan ya saka mata injin.

A bidiyon da aka gano a shafin BCR Worldwide na Instagram, maashin ya hau motar sannan ya tayar da ita.

Matashi na tuka motar kara
Matashi Ya Yi Amfani Da Katakai Wajen Kera Mota Harda Injin, Ya Tuka Abunsa a Bidiyo Hoto: Instagram/@bcrworldwide.
Asali: Instagram

Duk da cewar ba a san tsawon lokacin da ya dauka yana hada katakan don kera motar ba, wasu sun jinjinawa mutumin a kan wannan namijin kokari da ya yi.

Kara karanta wannan

"Wa Ya Aike Shi": Bidiyon Ango Ya Fadi Kasa Yayin Kokarin Daukar Matarsa Yayin Da Suke Rawa A Ranar Aurensu

Bidiyon motar da aka kera da kara

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Sai dai kuma wasu sun ce sam motar bai burge su ba domin dai gaba daya bai nuna wani hikima a ciki ba.

Duk da haka, mutumin ya tuka motar zuwa wani taron jama'a kuma ya burge mutane da dama da suka taru don kallon shi.

Bidiyon ya nuno shi yana tayar da motar kamar babur kafin ya tuka abun sa a bainar mutane. Bidiyon 'motar karan' mai kafafuwa hudu ya haifar da martani da dama.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

@donrabtob ya ceL

"Maza, wannan sabon abu ne. Mutum zai kauce cunkoson ababen hawa na Lagas."

@poolerena ya yi martani:

"A zahiri, da haka motoci suka fara. Kuma kan wannan nasara, mota abar hawa da daukar kaya ne."

@ddansinzu ta yi martani:

Kara karanta wannan

Matashiya Ta Kama Hauka Tuburan a Abuja, Ta Nemi Wata Angela Ta Rabu da Mijinta, Bidiyon Ya Yadu

"Duk da haka za su karbe shi na yin tasi."

@oluboriofficial ya ce:

"Hakan baya nufin ba zai biya yan daba kudin tikiti ba."

Matashi ya kera mota mai siffar G-Wagon

A wani lamari makamancin wannan, mun ji cewa jama'a sun jinjinawa wani matashi bayan sun ci karo da wata motar G-Wagon da ya kera da hannunsa.

An gano matashin yana tuka motar tasa a cikin harabar gidansu yayin da ahlinsu ke jinjinawa wannan kokari da ya yi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel