Babbar Magana Yayin da Aka Dauki Bidiyon Wasu ’Yan Sandan Kenya Na Yunkurin Aikata Fashi da Makami

Babbar Magana Yayin da Aka Dauki Bidiyon Wasu ’Yan Sandan Kenya Na Yunkurin Aikata Fashi da Makami

  • 'Yan sanda a kasar Kenya sun yi yunkurin yiwa wasu mutane biyu fashin miliyoyin shillin a kan titin Nairobi
  • Rahoto ya bayyana cewa, kyamarar CCTV ta nadi bidiyon yadda lamarin ya faru da kuma yadda mutanen suka sha dakyar
  • Ana yawan samun barna daga jami'an 'yan sanda bata-gari, suna saba dokar aikin al'umma, akan dauki mataki a kansu

Nairobi, kasar Kenya - Kyamarorin CCTV sun dauke lokacin da wasu jami'an 'yan sandan kasar Kenya ke yunkurin aikata fashin kudi kan wasu mutane a kasar.

Tuni dai kafafen yada labaran kasar suka yada bidiyon jami'an hudu, kuma an ga sadda suke kokari kwace shillin miliyan biyu daga hannun wasu mutane biyu.

A cewar rahoton BBC Hausa, kudaden da suke son kwacewar sun kai yawan adala 16,000 na Amurka, kuma hakan ya faru ne a titin birnin Nairobi na kasar.

Kara karanta wannan

Karshen alewa: 'Yan bindiga 5 da suka dade suna barna sun shiga hannun 'yan banga a jihar Arewa

'Yan sanda sun yi yunkurin yin fashi da makami
Babbar Magana Yayin da Aka Dauki Bidiyon Wasu ’Yan Sandan Kenya Na Yunkurin Aikata Fashi da Makami | Hoto: standardmedia.co.ke
Asali: UGC

An ruwaito cewa, mutanen biyu da 'yan sandan suka yi yunkurin zalunta ma'aikata ne a hukumar musayar kudin kasashen waje.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Hakazalika, an ce sun ciro kudin ne a banki sai kwatsam suka hadu da bata-garin 'yan sandan dak ke kokarin kwace kudin.

Yadda mutanen suka tsira, da yadda aka kama 'yan sandan

A tattaro cewa, mutanen biyu sun yi kururuwa, lamarin da ya dakatar da 'yan sandan daga aikata mummunan aikin da suka shirya yi.

Har ila yau, an ce an kama jami'an 'yan sandan hudu, kana an mika su kotu domin dandana fushin doka.

Ana yawan samun halayen rashin daa'a ga 'yan sanda a duniya, kama daga kasashen Turai har kan Nahiyar Afrika.

Akan bayyana daukar matakin kora ko dakatarwa ga jami'an da aka kama da aikata mummunan aiki irin wannan.

Kara karanta wannan

Hotunan Cikin Tamfatsetsen Gidan Da Ronaldo Ke Zama Tare Da Iyalansa a Saudiyya

Kalli bidiyon da aka yada:

Bidiyo ya nuna yadda 'yan sandan Najeriya ke shan varasa a bakin aiki, runduna ta yi martani

A wani labarin, an ga lokacin da wasu 'yan sandan Najeriya ke zaune suna cashewa, suna kwankwadar barasa a idon jama'a.

A lokacin da kwalbewa, an ga jami'an dauke da makamai, lamarin da ya jawo cece-kuce a Twitter.

Rundunar 'yan sandan ta ce sam ba halin jami'ai bane, za a nemo su a hukunta su daidai tsarin doka.

Asali: Legit.ng

Online view pixel