Rundunar ’Yan Sanda Ta Yi Martani Kan Wasu Jami’ai da Ke Kwankwadar Barasa a Bakin Aiki

Rundunar ’Yan Sanda Ta Yi Martani Kan Wasu Jami’ai da Ke Kwankwadar Barasa a Bakin Aiki

  • Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta bayyana cewa, ba daidai bane ake ganin jami’ai suna shan barasa a bakin aiki ba
  • Wannan na zuwa ne bayan da wani dan Najeriya ya yada bidiyo, ya tambayi bahasi kan shan barasa da wasu jami’ai ke yi a bakin aiki
  • A gefe guda, wani jami’in dan sanda ya bindige wata mata har lahira a ranar Kirsimeti saboda wasu dalilai mara tushe

Najeriya - Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Najeriya, Oluwayiwa Adejobi ya barranta da wasu jami’an ‘yan sanda da aka gani suna kwankwadar barasa a bakin aiki.

Wannan batu na nesanta rundunar ‘yan sanda da barin jami’ai su shan barasa a bakin aiki ya samo asali ne daga wani rubutun Twitter da wani ya tambaya ko hakan daidai ne a hukumar ‘yan sanda.

Kara karanta wannan

An kassara 'yan Boko Haram, an kamo wani kasurgumi daga cikinsu, an kashe 8

'Yan sanda na shan giya: Runduna ta yi martani
Rundunar ’Yan Sanda Ta Yi Martani Kan Wasu Jami’ai da Ke Kwankwadar Barasa a Bakin Aiki | Hoto: @MobilePunch
Asali: Twitter

Da yake martani, Adejobi ya bayyana cewa:

“A’a. Ba a shan barasa a bakin aiki.”

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Abin da aka gani suna aikatawa a cikin bidiyon

A bidiyon da aka yada, an ga lokacin dawasu jami’in da ke sanye da kakin ‘yan sanda ke ke shan barasa suna raha.

Hakazalika, an ga wani jami’i daga cikinsu yana rike da bindigar da gwamnati ke ba jami’an domin yin aikin kare ‘yan kasa daga mabarnata.

Ana yawan samun lokuta mabambanta a Najeriya da jami’an ‘yan sanda ke saba dokokin da suke da alaka da aiki, wanda hakan na iya kaiwa ga asarar rai ko barnar ta ganganci a cikin al’umma.

Oluwayiwa Adejobi na yawan amsa tambayoyin 'yan Najeriya tare da bayyana daukar mataki kan jami'an da aka gani suna saba dokokin hukumar.

Kalli bidiyon:

Kara karanta wannan

Dadi kashe ni: Bidiyon yadda yarinya ta shiga yanayi bayan kurban Fanta ya girgiza intanet

Barnar ganganci: Jami'in dan sanda ya bindige lauya har lahira

A baya kadan kunji cewa, wani jami’in dan sanda ya hallaka wata lauya mai suna Misis Omobolanle Raheem, a yankin Ajah da ke jihar Lagas a ranar Kirsimeti.

Rahoton da muka samo ya bayyana cewa, wani mataimakin sufeto ne ya dauki bindiga ya harbe wannan mata lauya kuma mambar kungiyar lauyoyi ta NBA.

Majiya ta shaida cewa, wannan lamari mara dadi ya faru ne a kasan gadar Ajah ta Legas lokacin matar ke kan hanyar dawowa daga coci a ranar kirsimeti tare da ahalinta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel