Shekarunta 23: Wani Mutum Ya Wallafa Hotunansa Da Wata Mata Mai Nakasa, An ce Sun yi Aure

Shekarunta 23: Wani Mutum Ya Wallafa Hotunansa Da Wata Mata Mai Nakasa, An ce Sun yi Aure

  • Wani mutum ya wallafa hotuna masu ban sha'awa tare da wata mata mai nakasa a kasar Ghana
  • Wanda ya wallafa hotunan ya ruwaito cewa pre-weddind ne kuma ana gab da daura musu aure
  • Legit ta gudanar da na ta bincike kan gaskiyar maganan auren dake tsakanin su

Kwanakin baya, wani faifan bidiyo ya yadu a kafar sadarwa ta TikTok inda wani mutumi ya dauki hoto tare da wata mata mai nakasa tamkar Amarya da Ango.

Labarin da ya yadu shine suna shirin yin aure inda mutane suka jinjina masa bisa amincewa ya aureta duk da nakasar da take fama da shi.

Wanda ya daura hoton ta TikTok Martin Edotse ya bayyana cewa aure suna gab da aure.

Amma Legit.ng ta gudanar da bincike kan bidiyon domin tabbatar da gaskiyar lamarin.

Kara karanta wannan

Lallai Fa: Bidiyon Wata Santaleliyar Budurwa Tana Fama Da Shanu Ya Girgiza Intanet

Vidal
Shekarunta 23: Wani Mutum Ya Wallafa Hotunansa Da Wata Mata Mai Nakasa, An ce Sun yi Aure
Asali: Original

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Binciken Legit

Da farko dai bidiyon ya dauki taken dake nuni ga cewa akwai alaka ta soyayya tsakaninsu kuma zasu yi aure.

Amma bincike ya nuna cewa mutumin da aka gani a bidiyon sunansa Clinton Yeboah, wani attajiri ne a kasar Ghana kuma ya shahara da taimakon masu nakasa.

Legit.ng ta tuntubesa kuma ya tabbatarwa wakilinmu da cewa ba shi da alaka ta soyayya da matar da aka gani tare da shi a hoton.

Sunanta Vida

A hirarsa da Legit.ng, Clinton wanda dalibi ne a jami'ar Ghana ya ce yanzu haka yana kula da nakasassu 50.

A cewarsa:

"Na kan shiga kauyuka domin samo nakasassu, marasa lafiya da talakawa mabukata taimako sannan sai in taimaka musu."
"Tana cikin masu nakasar da nike kula da su kuma yanzu haka ina kan gina musu gida mai daki biyu."

Kara karanta wannan

"Kullum Yana Zuwa" Bidiyon Alakar Wata Kyakkyawar Malama da Dalibinta a Ofis Ya Bar Mutane Baki Buɗe

Ba Mata ta bace

Legit.ng ta tambayi Clinton shin akwai alaka ta aure tsakaninsa da Vida, ya bayyana cewa:

"San babu. Kawai dai ina kokarin ganin cewa jama'a sun daina kyamatarta ne saboda sun fara kirarta mayya saboda irin halin da take ciki. Saboda haka ya zama wajibi in bayyanawa duniya cewa don an haifi mutum a haka, bai nufin mayya ce."

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel