Zan Siya Maka Mota: Matashi Ya Fashe Da Kuka Yayin da Diyarsa Ta Daukar Masa Alkawari a Bidiyo

Zan Siya Maka Mota: Matashi Ya Fashe Da Kuka Yayin da Diyarsa Ta Daukar Masa Alkawari a Bidiyo

  • Wani matashi dan Najeriya ya yi kicibis da karamar diyarsa tana shan chakulet a cikin kwaba kuma abun ya bashi mamaki
  • Ya tunkari yarinyar wacce nan take ta ba da hakuri kan abun da ta aikata bayan ta yi kokarin kare kanta da farko amma babu nasara
  • Sai dai kuma bata yi kasa a gwiwa ba ta yi alkawari cewa za ta siya masa mota duk da kasancewarta karama

Wani matashi dan Najeriya ya fashe da kuka bayan diyarsa karama ta yi alkawarin siya masa mota.

Mutumin ya kama yarinyar tsugune da gwangwanin milo tana sha a cikin kwabansu kuma nan take ya tunkareta.

Matashi da diyarsa
Zan Siya Maka Mota: Matashi Ya Fashe Da Kuka Yayin da Diyarsa Ta Daukar Masa Alkawari a Bidiyo Hoto: TikTok/@papa_daughter
Asali: UGC

Da take kare kanta, yarinyar ta bayyana cewa tana neman kayanta ne a ciki, amma kuma ga hannunta dumu-dumu a cikin milo.

Mahaifin nata ya fara yi mata fadan abun da tayi kuma nan take ta bayar da hakuri kafin ta yi alkawarin siya masa mota.

Kara karanta wannan

Ke duniya: Wani matashi ya yi tsaurin ido, ya sace mahaifinsa, an ba kudin fansa N2.5m

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Mutumin ya mayar da martani cewa zai siyawa kansa da kansa mota amma sai ya bar gabanta don zub da hawaye. Bidiyon ya haifar da martani a TikTok.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama’a sun yi martani a soshiyal midiya

Nuna Patrick655 ta ce:

“Mai sunana bama zuwa baya, dan Allah faaa za mu siya maka mota.”

Benedict ta ce:

“Gwanda ma ka rike yarinyar nan da tsauri. Kamar wasa-wasa. A haka yake farawa.”

Babygirl ta ce:

“Allah ubangiji ya kareta ya rayaka mafarkinta ya zama gaskiya ta siya motar nan kusa.”

Omotolani ta ce:

“Wannan abun dariya ne. Amma Ina fatan ka saita ta da kyau bayan bidiyon, saboda idan baka yi ba zata sake yi.”

Magidanci ya halaka matarsa saboda biredi

A wani labarin kuma, mun ji cewa wani magidanci mai suna Ndubisi Uwadiegwu, dan asalin jihar Enugu lakadawa matarsa, Ogochukwu Enene, duka har ta mutu saboda biredi.

Kara karanta wannan

Matashiya Ta Kama Hauka Tuburan a Abuja, Ta Nemi Wata Angela Ta Rabu da Mijinta, Bidiyon Ya Yadu

Kamar yadda rahotanni suka kawo, marigayiyar ta kasance yar kauyen Umuokpu, Awka a jihar Anambra, amma ta auri mijinta dan jihar Enugu.

Dan marigayiyar mai shekara 14, ya ce mahaifinsu ya bugi mahaifiyarsu da madubi har ta mutu, saboda ta bukaci ya siya musu biredi amma ya ce shi ba shi da kudi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel