Kayataccen Bidiyon Wata Budurwa Da Ta Yi Amfani da Maza a Matsayen Kawaye Ranar Biki

Kayataccen Bidiyon Wata Budurwa Da Ta Yi Amfani da Maza a Matsayen Kawaye Ranar Biki

  • Wata kyakkyawa ta zabi maida yan uwanta maza guda 5 a matsayin kawayen amarya a ranar daura aurenta
  • Yan uwan sun yi shiga mai ban sha'awa tare da yar uwarsu yayin da suka maye gurbin kawayen amarya
  • Masu amfani da kafafen sada zumunta sun bayyana ra'ayoyinsu game da lamarin, wasu sun yaba wa karamcin mazan

Domin kawatar da wurin shagalin bikin aurenta, wata kyakkyawar Amarya ta yi amfani da 'yan uwanta maza 5 a matsayin ƙawayenta.

A wani bidiyo da aka wallafa da shafin sada zumunta TikTok, ya nuna yadda 'yan uwan amaryar suka kewayeta suka dauke Hotonun masu ban sha'awa.

Maza a matsayin kawayen Amarya.
Kayataccen Bidiyon Wata Budurwa Da Ta Yi Amfani da Maza a Matsayen Kawaye Ranar Biki Hoto: @Bless_irene
Asali: UGC

Yan uwan budurwar sun yi shigar kaya masu kama da Alfarari yayin da ita kuma amarya ta sa kaya masu kalar kore mai duhu-duhu. Mazan sun taka rawa a matsayin kawayen amarya yadda ya kamata.

Kara karanta wannan

Bayan Sun Shafe Shekaru 10 da Aure Harda Yara 2, Ma'aurata Sun Gano Cewa Iyayensu Daya

Da yawan matan da suka yi martani kan Bidiyon sun bayyana sha'awarsu na yin makamancin haka a ranar daura aurensu yayin da wasu kuma suka yi tsokaci game da shigar yan uwan amarya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kalli bidiyon shagalin bikin a nan

Martanin mutane kan matakin amarya

@Massage therapist ya ce:

"Ta tsira daga duk wani tuggu, kishi, hassada da maitar da ake fama da ita daga kawaye."

Ita kuwa Djdlite2 abun ya burgeta inda ta bayyana cewa:

"Ina ma ace ina da yan uwa maza da yawa ta yadda nima idan aure na ya zo na dauke su a matsayin kaawayen Amarya."

Kysh Official ya ce:

"Na rantse da Allah ya zama tilas Ango ya kula sosai da zuciyar wannan amarya da ya aura."

user309291711122 ya rubuta ra'ayinsa da cewa:

"Wannan shi ne abinda ya dace saboda ba zasu bayyana surar jikinsu ga mijinta ba su maza ne, Allah ya miki Albarka yar uwa."

Kara karanta wannan

"Kullum Yana Zuwa" Bidiyon Alakar Wata Kyakkyawar Malama da Dalibinta a Ofis Ya Bar Mutane Baki Buɗe

A wani labarin kuma Wata Sabuwar Amarya ta shiga tashin hankali yayin da ta kama Ango na lalata da kanwarta a gado kwana huɗu da aurensu

Sabuwar amaryar da abun ya sosa wa zuciya, tace lamarin ya taɓa ta yadda ta koma Otal na tsawon mako ɗaya ba wanka da yawo don komai ba ya mata daɗi.

Haka zalika ta nuna ba zata taɓa yafe musu ba kuma ta garkame lambobin mahaifiyarta da surukarta saboda sun nemi ta kai zuciya nesa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel