Bidiyon Wani Dalibi Wanda Yake Zuwa Ofishin Kyakkyawar Malamarsu Ya Ja Hankali

Bidiyon Wani Dalibi Wanda Yake Zuwa Ofishin Kyakkyawar Malamarsu Ya Ja Hankali

  • Wata Malamar makaranta ta wallafa bidiyon dalibinta Namiji wanda ba ya iya zama ba tare da ya je Ofis ya ganta ba
  • A bidiyon da ta dauka, an ga dalibin na fara'a da ke nuna yana gamsuwa idan yana tare da zankadadiyar malamar ta su
  • Mutane da yawa sun yi tsokaci a kan bidiyon wasu sun jinjina wa budurwar bisa gina kyakkyawar alaƙa da dalibinta

Wata kyakkyawar Malamar makaranta @Audriwill_ ta dauki Hoto mai magana wanda ya shafi wani dalibinta namiji da ke yawan kawo mata ziyara Ofis.

Bidiyon ya nuna yaron na shiga yanayin farin ciki na annashuwa duk lokacin da yake tare da Malamar ta su. Tace ta kirga lokuta Takwas da ya zo Ofishinta a rana ɗaya.

Alakar Malama da Dalibinta.
Bidiyon Wani Dalibi Wanda Yake Zuwa Ofishin Kyakkyawar Malamarsu Ya Ja Hankali Hoto: @audriwill
Asali: UGC

Dalibin na jin dadi idan suna tare

Kara karanta wannan

Bidiyon Budurwa Tana Rafsar Kuka Bayan ta Debo Ciki, Tana Neman Yadda Za ta Sanarwa Mahaifiyarta

A wasu lokuta kamar yadda Bidiyon ya nuna, Dalibin ya kan tika rawa a gaban malamar kuma ya kira ta da kyakkyawa mai kyaun sura. Ya kan ji daidai idan suna tare.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wasu da yawa da suka maida martani sun ce yaron na jin natsuwa idan yana tare da Malamar. Ga dukkan alamu alaƙar dalibin da malamarsa ta yi karfi.

Kalli bidiyon su tare da juna

A yanzu da muke haɗa maku wannan rahoton, kusan mutane 2,000 suka bayyana ra'ayoyinsu kan Bidiyon yayin da sama da mutane 200,000 suka kalla.

Abinda jama'a ke cewa kan batun

Legit.ng Hausa ta tattaro maku wasu daga cikin martanin jama'a, gasu kamar haka:

A Pretty Hot Mom tace:

"Ga dukkan alamu yana bukatarki fiye da yadda kike tunani."

Rocky Roulette ta ce:

"Babu tantama wannan dalibin zai dawo don ya ganki bayan ya kammala karatu."

Kara karanta wannan

Bidiyo: Dumu-dumu Saurayi Ya Kama Budurwarsa Tana Masa Sata, Tayi Borin Kunya Kiri-kiri

KiaG ya ce:

"Wannan ai kanina ne kuma yana abu kamar yadda ya saba a gida."

Imani ta ce:

"Wannan hanaya ce ta da zaki san kina da kwarewa kan aiki kuma kina taka rawa rayuwarsu."

A wani labarin kuma Wani Mutumi Ya Ziyarci Gidan Tsohuwar Matarsa, Ya Kama Tube Kaya a Gaban 'Diyarsa a Bidiyo

Da farko dai mutumin wanda ke cikin farin ciki ya fara yabon dakin tsohuwar matar wacce suka ravu ba da jimawa ba daga bisnia ya fara cire kaya a gaban yarsa.

Diyarsa ta yi mamaki matuka yayin da ta kalli yadda mahaifinta ke kokarin tube kayansa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel