Matar DG na DSS ta Hana Abba Gida-Gida Hawa Jirgin da Zata Hau, Ta Sa an Lakadawa Hadiminsa Dukan Mutuwa

Matar DG na DSS ta Hana Abba Gida-Gida Hawa Jirgin da Zata Hau, Ta Sa an Lakadawa Hadiminsa Dukan Mutuwa

  • An yi karamar dirama tsakanin Aisha Bichi, Matar DG na DSS da Abba Yusuf, ‘Dan takarar gwmamban Kano a jam’iyyar NNPP, a filin jirgin sama na Malam Aminu da ke Kano
  • An tattaro yadda tawagar Abba ta tare Bichi daga shiga falon muhimman jama’a wanda hakan yasa jami’an tsaro da hadimansa suka yi arangama
  • Cigaba da hargitsi tsakaninsu ne yasa Bichi ta sa aka kama Abba Yusuf tare da sa a lakadawa hadiminsa da ke nadar lamarin dukan kawo wuka

Kano - An yi kwarya-kwaryar dirama a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano yayin da Aisha Bichi, matar darakta janar na hukumar tsaro na farin kaya, DSS, ta hana Injiniya Abba Yusuf, 'dan takarar gwamnan jihar Kano a NNPP, hawa jirgin sama.

Abba Gida-gida da Aisha Bichi
Matar DG na DSS ta Hana Abba Gida-Gida Hawa Jirgin da Zata Hau, Ta Sa an Lakadawa Hadiminsa Dukan Mutuwa. Hoto daga SaharaReporters.com
Asali: UGC

Daily Trust ta tattaro cewa, lamarin ya fara ne yayin da tawagar Yusuf ta dakatar da ta Bichi daga shiga falon jama'a masu muhimmanci.

Kara karanta wannan

Adamawa Ta Cika Ta Batse Yayin da Shugaba Buhari Ya isa Mahaifar Atiku Don Yakin Neman Zaben APC

Wannan an tattaro yasa jami'an tsaronta suka shiga lamarin tare da buda hanya wanda a hakan ne aka yi cacar baki tsakanin jami'an tsaron da hadiman 'dan takarar gwamnan.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Wata majiya wacce ta bukaci a boye sunanta ta bayyana yadda lamarin ya koma cacar baki tsakanin Yusuf da Bichi yayin da ta tunkaresa kan lamarin.

"Lamarin ya kara kamari yayin da ta sanar da Abba cewa ba zasu shiga jirgi daya ba kamar yadda aka tsara tun farko kuma ta hango daya daga cikin hadimansa mai suna Garba Kilo yana nadar abinda ke faruwa."

- Majiyar tace.

Kilo wanda jami'an tsaro suka lakada masa duka bisa umarnin matar Bichi, an mika shi asibitin koyarwa na Aminu Kano don samun taimako.

"Sun lakadawa Kilo mugun duka kuma wannan ne yasa Abba ya jaddada cewa sai ya shiga jirgi daya da ita kamar yadda tsarin yake tun farko, wanda hakan ya fusata ta kuma ta bukaci a kama shi,"

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: An Kama Wani Mai Hannu a Garkuwa Fasinjojin Jirgin Kasa a Najeriya, Ya Fara Bayani

- Majiyar tace.

An tattaro cewa, an sake turo wasu jami'an tsaron farin kayan wadanda suka tsare 'dan takarar gwamnan har sai da jirgin matar Bichi ya tashi.

Amma wani babban jami'in DSS wanda ya ke wurin da lamarin ya faru amma ya bukaci a boye sunansa, yace dukkan lamarin za a iya guje shi kuma ba daidai bane idan aka kwatanta matar uban gidansa da masifaffa.

Yayin da Sanusi Bature, kakakin jam'iyyar NNPP ba a samesa ba don tsokaci, kakakin DSS, Peter Afunanya ya sanar da Daily Trust cewa labarin dukan da jami'ansu suka yi wa wani ba gaskiya bane kuma tura jami'ai suka yi kamar yadda dokar aikin ta tanadar.

Yace rahotannin an kama 'dan takarar gwamnan, gulma ce da bata da tushe kuma bata bukatar hukumar ta mayar da hankali kai.

Sarkin Kano ya aura matata biyu

A wani labari na daban, Mai Martaba Alhaji Aminu Ado Bayero, Sarkin Kano, ya aura tsoguwar budurwarsa, Hauwa Adamu Abdullahi Dikko wacce aka fi sani da Hajiyayye.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Hukumar NRC Ta Rufe Tashar Jirgin Kasa da Yan Bindiga Suka Kai Hari

An daura auren ne a franar Juma'a da ta gabata babu wasu shagulgula ko bidirin da aka saba na aure.

Asali: Legit.ng

Online view pixel