Budurwa ta Debo Ciki, Tana Kuka a Bidiyo Kan Bata San Yadda Za ta Sanar da Mahaifiyarta ba

Budurwa ta Debo Ciki, Tana Kuka a Bidiyo Kan Bata San Yadda Za ta Sanar da Mahaifiyarta ba

  • Wata budurwa 'yar Najeriya ta bar mutane cike da mamaki da bidiyon dake bayyana yadda take dauke da juna biyu
  • Budurwar ta zubda hawaye yayin da ta tabbatar da tana dauke da juna biyu, tare da tunanin yadda za ta fadawa mahaifiyarta
  • Mutane da dama a yanar gizo sun sha mamaki game da bidiyon nata, yayin da suka yi ta tsokaci mai ban dariya, inda wasu ke taya ta murna

Wata budurwa mai karancin shekaru ta koka a yanar gizo bayan gano yadda take dauke da juna biyu, sannan tana sa ran samun rabo.

Budurwa mai ciki
Budurwa ta Debo Ciki, Tana Kuka a Bidiyo Kan Bata San Yadda Za ta Sanar da Mahaifiyarta ba. Hoto daga TikTok/@_na_nah
Asali: UGC

A bidiyon TikTok din, an ganta tana zubda hawaye tare da mamakin yadda za ta shaidawa mahaifiyarta labarin.

An ga yadda take rike da wata takardar da tayi amfani da ita wajen tabbatar da tana dauke da juna biyun. Ta koka matuka game da yadda ta fara sabuwar shekara da juna biyu.

Kara karanta wannan

Bidiyon Magidancin da ya Gane Matarsa na da Kanjamau Bayan Shekara 3 da Aurensu, yace Yarda ce ta Janyo Masa haka

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Dubi da abun da na fara sabuwar shekarar nan fa.”

- Tayi tsokaci karkashin bidiyon.

Bidiyon da ta wallafa ya janot cecekuce a yanar gizo yayin da 'yan soshiyal midiya suka bayyana ra'ayoyinsu game da gane tana da juna biyun.

Tsokacin jama'a

mama_esosa ta ce:

"Ina taya ki murna, ina rokonki kada kiji haushi. 'Da shi ne babban arzikin da za a azurta mace da shi. An miki babbar kyauta."

kindandgreat ya ce:

"Yarinya ina taya ki murna, abun farinciki ne, wasu mutane na nema ido rufe, ki goge hawayen ki."

Amarachi ta ce:

"Hakan ya miki dadi ai arziki ne, idan mutumin da ya dirka miki cikin na tare dake."

Tunde ariyo ya ce:

"Ki ce mata mala'ika ne ya dirka miki cikin."

Kara karanta wannan

Matashiya Ta Kama Hauka Tuburan a Abuja, Ta Nemi Wata Angela Ta Rabu da Mijinta, Bidiyon Ya Yadu

RealRitaPatson ta ce:

"Ki fara sanarwa saurayin ki ji daga gareshi... amma kada ki sare a komai.. Ubangiji zai duba lamarinki."

user6065239895808 ya ce:

"Wayyo Ubangiji, yaushe nima zan samu nawa juna biyun? Ku taya ni addua har na gaji da azumi."

zenith's peace ta ce:

"Ki yi bayani kamar yadda ki ka yi mana bayani a nan, (ba a nake).
"Iyaye mata na son hakan, ki fada mata, ko kuma idan kina da babbar yaya wacce ta san yadda za ta taimakeki."

Bidiyon gurgu mai kafa daya yana tuka keke cike da kwarewa

A wani labari na daban, wani bawan Allah yayi godiya da yake da cikakkiyar lafiya kuma babu nakasa bayan ya ga gurgu mai kafa daya yana tuka keke.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Online view pixel