Kamfanin da Ya Buga Sabbin Naira Ya Bayyana Dalilin da Yasa Launi Kadai Aka Sauyawa Kudin
- Fitaccen kamfanin buga takardu a Najeriya, Nigerian Printing and Minting Plc ya sake bayyana wasu sarkafe-sarkafen tsaro da jikin sabbin kudin Najeriya
- Kamfanin ya bayyana cewa, yana son warware abin da ya shigewa ‘yan Najeriya dubu ne game da ingancin sabbin Naira
- Ya bayyana cewa, kodar da launin kudin na daga cikin surkullen tsaron da ya yi tunanin sakawa a jikin sabbin Naira
FCT, Abuja - Nigerian Security Printing and Minting Plc, fitaccen kamfanin buga takardu a Najeriya ya yi karin haske game da surkullen tsaron da ke cikin sabbin kudaden Naira da ya buga kwanan nan.
Ya bayyana cewa, wasu daga abubuwan da ‘yan Najeriya ke kokawa a kai game sabbin kudin ba komai bane face wata dabara ta ba kudaden kasar kariyar tsaro.
Wannan batu na zuwa ne daidai lokacin da ‘yan kasar ke ci gaba da bayyana damuwa game da yadda sabon sauyin Naira ya zo da abubuwan da ba a yi tsammani ba.
Kamfanin ya yi karin haske game da sabbin kudaden ne a ranar 6 ga watan Janairun bana a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Manajan Daraktansa, Ahmed Halilu.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
'Yan Najerya sun damu da launin sabbin Naira
A cewar sanarwar, kamfanin ya gano yadda ‘yan Najeriya suka damu, kuma suke yada bidiyo da hotunan da ke dasa ayar tambaya kan ingancin kudaden a kafafen sada zumunta.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa, kamfanin ya ce akwai bukatar ‘yan Najeriya su fahimci cewa, an yi komai daidai tsari kuma yadda zai gamsar da ‘yan kasar.
Hakazalika, kamfanin ya ce ya shafe shekaru yana aiki tare da biyawa ‘yan kasar bukata wajen yin abubuwan da suka shafi kudi ta hannun CBN tun 2014.
A cewar kamfanin, a yanzu Najeriya bata amince da batun shigowa ko buga kudadenta a kasashen waje, don haka ta kawo hanyar kirkira da buga kudin a cikin gida.
Launi kadai aka sauya, ga dalili
A cewar sanarwar da kamfanin ya fitar, kudaden dai kamar na da ne, kawai sauya musu launi aka yi ba tare da sauya komai ba kamar yadda wasu suka yi tsammani.
Ya kara da cewa, abu mafi muhimmanci da ‘yan Najeriya ya kamata su fahimta shi ne, sabbin kudin basu da nauyi a sadda aka ba da su, amma za su yi nauyi a lokacin da suka gwamu da dattin hannun jama’a ta dalilan musayar mallaka.
Hakazalika, kamfanin ya ce an yi amfani da tawadda na musamman wajen gyara da cire hotunan da ke jikin kudin daidai bukata, don haka za a saba da kudaden na kusa
A bangare guda, kamfanin ya ce kudaden suna daidai da tsari da zubin kudaden sauran kasashen duniya, don haka ingancinsu na kasa da kasa ne, rahoton This Day.
Daga karshe ya gargadi 'yan kasar da su daina gwajin ingancin kudin ta hanyar tsoma kudin a ruwa.
‘Yan Najeriya na ci gaba da ciza yatsa da kuma tura baki game da sabbin kudin tun bayan da suka fara yawo a Najeriya a ranar 15 ga watan Disamban bara.
Wasu sun yi imani da cewa, sabbin kudaden basu da wani inganci kuma suna wankewa da zarar sun gamu da ruwa ko wani abu mai ruwa-ruwa.
Asali: Legit.ng