Akwai Isassun Sabbin Kudi A Bankuna, Bamu Hana Badasu a Kanta Ba: CBN Tayi Martani

Akwai Isassun Sabbin Kudi A Bankuna, Bamu Hana Badasu a Kanta Ba: CBN Tayi Martani

  • CBN ya ce yan Najeriya zasu fara samun sabbin kudi a na'urorin ATM a fadin kasa daga yanzu
  • Bankin ya jaddada cewa kowa ya kai tsaffin kudadensa banki nan da makonni uku kada su zama banza
  • Gwamnatin Najeriya ta sauya takardun kudinta Naira N200, N500 da N1000 don wasu dalilai 4

Abuja - Babban bankin kasa CBN ya yi watsi da rahotannin cewa ana samun karancin sabbin tsabar kudi a fadin bankunan Najeriya, rahoton ThisDay.

Bankin ya ce akwai akwai isassun kudi a bankuna a fadin kasa kuma tana kan bakanta na daina amfani da tsaffin takardun dake yawo hannun mutane ranar 31 ga Junairu, 2023.

CBN ya kara da cewa shi bai hana bankuna baiwa mutane sabbin kudi a kan kanta ba kawai dai an umurci bankunan ne su kara adadin kudaden da suke zubawa a na'urar ATM saboda sabbin takardun suyi yawa hannun jama'a.

Kara karanta wannan

Toh fa: Gwamnan APC ya yi gargadin karshe, ya fadi abin da zai yiwa duk bankin ya ki tsoffin Naira

Naira
Akwai Isassun Sabbin Kudi A Bankuna, Bamu Hana Badasu a Kanta Ba: CBN Tayi Martani
Asali: UGC

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Bankin yace daga yanzu sabbin kudade kadai bankuna zasu rika zubawa a na'urorinsu na ATM dake fadin kasa.

Diraktan yada labaran bankin, Mr Osita Nwanisobi, ya bayyana cewa bankin ya yi wasu shirye-shirye na tabbatar da yaduwar kudaden a cikin gari.

Yace:

"Ko kadan ba ce a daina bada kudi a bakin 'kanta' ba."
"Mun zanna da bankunan kuma muka yi ittifakin cewa a fara sanya sabbin kudaden cikin ATM saboda mutane su samu kuma ya yadu."
"Lallai wannan umurni ne. mun yi zaman ne saboda mutane na korafin cewa ba su ganin sabbin kudaden. Kuma hakan bai nufin bankuna ba zasu iya bada kudi a 'kanta' ba."
"Muna da isassun kudade, kuma za'a iya amfani da tsaffin kudi har zuwa ranar 31 ga Junairu."

Babban Bankin Kasa CBN Ya Hana Cire Sabbin Kudi Akan Kanta Sai Dai A ATM kawai

Kara karanta wannan

Rikicin Naira: Masu gidajen mai sun ki karbar tsoffin kudi duk da umarnin CBN, sun fadi dalili

Babban bankin kasa CBN, ya umarci bankunan kasuwancin kasar nan da su daina bayar da sabbin kudade akan kanta, sai dai a injinun cirar kudi na ATM.

Dakar sannan ta kara jaddadawa bankunan kan su kiyaye da umarnin tare da aiwatar da shi a hada-hadar kudi.

yayin da yake bayyanawa wakilin jaridar The Cable, mai magana da yawun Osita Nwasinobi yace dokar ta fara aiki nan take.

Asali: Legit.ng

Online view pixel