Wani Magidanci, Nuhu Usman, Ya Bindige Matarsa Har Lahira A Bauchi

Wani Magidanci, Nuhu Usman, Ya Bindige Matarsa Har Lahira A Bauchi

  • Wani magidanci mai suna Nuhu Umar Usman ya fada hannun yan sanda kan zarginsa da kashe matarsa a gida
  • Binciken yan sanda ya nuna cewa matar ta tashi cikin dare ta shiga bandaki yayin da suke barci da mijin, da dawowarta ya harbe ta
  • Rahoto ya nuna cewa mijin yana tsammanin babban dansa ne da ya yi barazanar zuwa ya masa lahani bayan sabani da suka samu

Jihar Bauchi - Wani mutum dan shekara 40, Nuhu Usman, mazaunin kauyen Dangarga a Burra a karamar hukumar Ningi na jihar Bauchi ya bindige daya cikin matarsa biyu ya halaka ta.

Kakakin yan sandan jihar Bauchi, Ahmed Wakil, wanda ya sanar da hakan ranar Juma'a ya ce an garzaya da wacce abin ya faru da ita ya ce an garzaya da ita asibiti, likitoci suka tabbatar ta rasu.

Kara karanta wannan

Yadda Matashi Ya Kera 'Motar Kara' Harda Sa Mata Injin, Ya Tashe Ta a Cikin Bidiyo

Taswirar Jihar Bauchi
Wani Magidanci Ya Bindige Matarsa Har Lahira A Jihar Bauchi. Hoto: @MobilePunch.
Asali: UGC

Ya zaci dansa ne da ya yi barazanar zai masa lahani

An ce wanda ake zargin ya ajiye bindigansa kusa da shi lokacin zai kwanta barci, ya yi tunanin babban dansa da ke fushi da shi ne ya taho ya cutar da shi, rahoton LIB.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Usman yana barci tare da matarsa kuma ta tashi ta tafi bandaki bayan dawowanta, ya yi tsammanin babban dansa ne ya taho ya cutar da shi, sai ya harbe ta da bindiga a ciki.

Wani sashi na sanarwar ta ce:

"Binciken farko ya nuna wanda ake zargin ya kwanta daki daya da wacce ta rasu a daren, wanda ake zargin yana da mata biyu da yaya shida.
"An yi rikici tsakanin matan har ta kai babban dansa yana jin haushin mahaifinsa ya kuma yi barazanar yi masa lahani.

Kara karanta wannan

Ba zama: Legas ta rikici, direba ya banke dan sanda ya fece, runduna ta fusata

"Kafin nan, babban dan ya yi wa mahaifinsa barazana. Hakan yasa shirya bindigansa ya ajiye ta kusa da shi cikin dare, yana jiran tsammanin zuwan wani, ta yiwu babban dansa."

Kwamishinan yan sandan jihar CP Aminu Alhassan ya bada umurnin a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu da zarar an kammala bincike.

Kishi ya sa wata matar aure halaka yar kishiyarta a Katsina

A wani rahoton, yan sanda a jihar Katsina sun kama wata Aisha Abubakar yar shekara 38 kan zargin kashe yar kishiyarta.

Kakakin yan sandan jihar, Gambo Isah ne ya bayyanawa yan jarida hakan a ranar Talata a Katsina.

A cewarsa, ana zargin Aisha ta bawa yarinyar yar shekara hudu guba a cikin abinci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel