Ina Ma Ace Na Yi Aure da Wuri: Magidanci Dan Shekaru 50 Ya Koka Yayin da Yake Tafiya da Diyarsa Mai Shekaru 4

Ina Ma Ace Na Yi Aure da Wuri: Magidanci Dan Shekaru 50 Ya Koka Yayin da Yake Tafiya da Diyarsa Mai Shekaru 4

  • Wani magidanci ya ce ya so ace ya yi auren wuri da matarsa saboda ya so ace shekarun yaransa ya fi yadda suke
  • A wani bidiyo, an gano magidancin mai shekaru 50 yana tafiya tare da diyarsa wacce ta cika shekaru hudu a kwanan nan
  • Da suke martani ga bidiyon da ya yadu wasu jama'a sun shawarce shi da ya karbi kaddararsa a yadda ta zo masa yayin da wasu suka rarrashe shi

Wani bature mai shekaru 50 a duniya ya bayyana babban nadamarsa a rayuwa na rashin yin aure da wuri a rayuwa.

A wani bidiyo da ya yadu, an gano mutumin yana tafiya tare da kyakkyawar diyarsa mai shekaru hudu kuma yana fatan ina ma ace ya yi aure da wuri.

Uba da 'ya
Ina Ma Ace Na Yi Aure da Wuri: Magidanci Dan Shekaru 50 Ya Koka Yayin da Yake Tafiya da Diyarsa Mai Shekaru 4 Hoto: @cindycamponovo/TikTok
Asali: UGC

Matarsa ta wallafa bidiyon a dandalin soshiyal midiya sannan ta bayyana yadda mijinta ya ke damuwa sosai a kan rashin yin aure da wuri.

Kara karanta wannan

Dandazon Masoya Sun Dira Ribas a Fatakwal Yayin Da Portable Ya Yi Waka A Tsakiyar Rafi, Bidiyon Ya Bazu

Ta ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Mijina ya ce yana ji ina ma ace ya hadu da ni da wuri a rayuwa. Ya ce kasancewarsa uba ga yarinya yar shekaru hudu na sanya shi bakin ciki. Na ce masa idan da ya hadu da ni da wuri da an kama shi."

Jama'a sun yi martani

Jama'a sun tausayawa mutumin yayin da wasu suka shawarce shi kan ya yarda da kaddarasa.

@luzimarq ta ce:

"Saurayina shekarunsa 45 - ni shekaruna 30. Bana so ya zama uba a lokacin da ya tsufa amma kuma ban shirya zama uwa ba."

@marla_kay_leigh ta bayyana cewa:

"Ana rikona ne, mahaifina shine kakana. Na kan ji bakin ciki idan na tuna cewa ba zan dade da shi ba, shekaruna 15 sannan shi shekarunsa 71. Shi kadai nake da shi a rayuwa."

@lovehatedream ta rubuta:

Kara karanta wannan

Bidiyon Matar Aure Tana Gaggawar Ba Miji Abinci a Baki Kada ya Makara Aiki ya Janyo Cece-kuce

"Mahaifina ya haifeni yana da shekaru 48, ina matukar bakin ciki ganin cewa yana tsufa. Amma har yanzu ina kaunarsa da dukkan zuciyana."

Kalli bidiyon a kasa:

Bidiyon karamar yarinya tana sharban bacci a tsaye ya ba da mamaki

A wani labari na daban, jama'a sun tofa albarkacin bakunansu bayan cin karo da bidiyon wata karamar yarinya tana sharar bacci a tsaye.

An dai gano yarinyar tsaye tana bacci tamkar wacce ta samu katifa lamarin da ya baiwa mutane mamaki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel