Ki Kyale Mun Mijina: Matashiya Ta Haukace a Abuja, Ta Nemi Angela Ta Bar Mata Mijinta, Bidiyon Ya Yadu

Ki Kyale Mun Mijina: Matashiya Ta Haukace a Abuja, Ta Nemi Angela Ta Bar Mata Mijinta, Bidiyon Ya Yadu

  • An sha wata yar dirama a mararrabar Jahi, Abuja yayin da wata mata ta kama hauka tuburan sannan ta fara wasu kalamai masu ban al'ajabi
  • Matar mai lalurar tabin hankalin ta yi kira ga wata Angela da kyale mata mijinta yayin da ta kuma zargeta da jefata cikin halin da take a yanzu
  • Wani ganau wanda ya wallafa bidiyon ya yi kira ga jama'a da suka santa ko yan uwanta da su ziyarci ofishin yan sanda na Mabushi

Abuja - Mutane sun cika da mamaki bayan ganin wata mata da ba a san kowacece ba ta kama hauka tuburan a mararrabar Jahi da ke Abuja.

Wani ganau mai suna Philip Kwaghterna Zakpe ya wallafa bidiyon al'amarin a Facebook, yana mai cewa ta ambaci wata Angela.

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Kashe Dan Siyasa Da Wasu Mutane Uku a Wata Jahar Kudu

Matashiya ta kama hauka
Ki Kyale Mun Mijina: Matashiya Ta Haukace a Abuja, Ta Nemi Angela Ta Bar Mata Mijinta, Bidiyon Ya Yadu Hoto: Philip Kwaghterna Zakpe
Asali: Facebook

Philip ya kara da cewar babu wani katin shaida a tattare da ita ko waya. Ya bukaci mutanen da suka santa su ziyarci ofishin yan sanda na Mabushi.

Ya rubuta:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Na ci karo da wannan al'amari a mararrabar Jahi kafin Next Cash and Carry. Tana ta nuna hauka tuburan sannan tana kiran Angela. Bata da wani katin shaida a tattare da ita. Babu waya, babu ID...
"Idan ka gane ta ko ka san wani na kusa da ita...ka sanar da mai shi ya je ofishin yan sandan Mabushi."

A bidiyon, an gano matar ta daura laifin halin da take ciki kan Angela sannan ta roketa a kan ta bar mata mijinta.

Jama'a sun yi martani

Winifred Viashima ta ce:

"Duk ku kwantar da hankalinku...Na ga wannan abun jiya abun da matar ke fadi kawai shine Angela sannan tana ta ihu wasu bayin Allah sun dauketa zuwa cikin Jahi ko wani zai gane ta amma babu wanda ya san ta...Matashiyar budurwa ce bana tunanin ma ta yi aure..."

Kara karanta wannan

2023: Mata Za Su Samu Kudi a Karkashin Gwamnatin Mijina, In ji Matar Obi

Chidinma Eze ta ce:

"Mata na tsantsar hauka da wannan lamari na kwace miji. Dan Allah mu shirya zuciyarnmu ya iya daukar abubuwa masu muni don idan suka yaudareka kaduwar da fushin ba zai taba kwakwalwarka ba. Mata don Allah ku dunga lura da zukatanku."

Elizabeth Udeh a ce:

"Abun da mata ke gani saboda wani miji, ya ku mata ku kyale wadannan mutanen sannan ku fuskanci gabanku yanzu kuma diyar wani ce kuma uwar wani ba wai matar aure ba kawai."

A wani labari na daban, mun ji cewa hayakin gawayi ya yi ajalin wani miji da matarsa suna tsaka da bacci a jihar Kano.

Asali: Legit.ng

Online view pixel