Zamfara: ‘Yan Sanda Sun Halaka ‘Dan Bindiga, Sun Kama Mutum 6 da Ake Zargi

Zamfara: ‘Yan Sanda Sun Halaka ‘Dan Bindiga, Sun Kama Mutum 6 da Ake Zargi

  • A samame daban-daban, jami'an tsaro sun yi nasarar cafke wasu da ake zargi da ta'addanci, garkuwa da mutane, gami da satar shanu a fadin jihar Zamfara da kewaye
  • Kamar yadda kakakin 'yan sandan jihar, Muhammad Shehu ya bayyana a ranar Alhamis, jami'an sun yi nasarar bayan samun kiran gaggawa game da yadda 'yan ta'adda ke shirin tare titi
  • Haka zalika, yayin bincikar lamarin, wasu daga cikin 'yan ta'addan sun fallasa yadda suke bin tawagar Bello Turji, Halidu Kacahalla da Malam Tukur, sannan suke addabar Zamfara, Katsina, Kaduna da jihar Neja

Zamfara - Rundunar 'yan sandan jihar Zamfara ta sheke wani 'dan bindiga gami da yin ram da wasu shida da ake zargi da ta'addanci, garkuwa da mutane da satar shanu.

‘Yan sanda
Zamfara: ‘Yan Sanda Sun Halaka ‘Dan Bindiga, Sun Kama Mutum 6 da Ake Zargi. Hoto daga punchng.com
Asali: UGC

Hakan yazo ne a wata takarda da kakakin rundunar 'yan sandan, Muhammad Shehu ya fitar ranar Alhamis a Gusau, jaridar Punch ta rahoto.

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Kashe Dan Siyasa Da Wasu Mutane Uku a Wata Jahar Kudu

Shehu ya kara da bayyana yadda jami'an rundunar suka dakile harin 'yan bindigan gami da gano bindigu kirar AK47 biyu, harsasai masu lingimi 104 da carbin harsasai 2 da layu.

"A ranar 1 ga watan Janairu, jami'an 'yan sanda yayin sintiri wuraren titin Gusau zuwa Dansadau, suka samu kiran gaggawa game da shirin da 'yan bindiga suke na tare titin gami da kai hari ga masu wucewa tare da aukawa wasu kauyuka.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Ba tare da jinkiri ba, aka shirya tawagar zuwa wurin, inda suka yi musayar wuta.
"An yi nasarar sheke 'dan bindiga daya gami da dakile harin saboda tsananin luguden wutar da jami'an 'yan sandan suka yi musu, hakan yasa suka yada makamansu tare da tserewa zuwa daji, wata kila da raunukan harsasai.”

- A cewarsa.

A cewarsa, 'yan jami'an suna aiwatar da sintiri don samar da natsuwa, inda suka dakata gami da amfani da bayanan sirrin da suka samu wanda yayi sanadin cafke biyu daga cikin wadanda ake zargi da satar mutane da shanu.

Kara karanta wannan

Hawaye Sun Kwaranya Yayin da Dan Sanda Ya Kashe Matasa 2 Tare Da Jikkata Wasu 3 a Wata Jahar Arewa

"Yayin da aka tuhumesu, wadanda ake zargin sun fallasa yadda suke garkuwa da mutane tare da satar shanu a jihohin Zamfara, Katsina, Kaduna, Neja.
"Haka zalika, wadanda ake zargin sun bayyana yadda suke tawagar gawurtaccen shugaban 'yan ta'addan nan, Bello Turji.
"A ranar 1 ga watan Janairu, misalin karfe 1:30 na dare, jami'an 'yan sandan yayin sintirin tabbatar da tsaro, sun yi ram da wata tawagar gawurtaccen shugaban 'yan ta'addan nan wanda aka fi sani da Halilu Kachalla."

- A cewarsa.

"Har ila yau, ranar 2 ga watan Janairu misalin 12:15 na dare, jami'an 'yan sandan dake aiki wuraren titin Gusau zuwa Tsafe yayin wani sintiri sun cafke wasu da ake zargi da ta'addanci.
"Yayin bincike, wadanda ake zargin sun fallasa yadda suke cikin tawagar 'yan bindigan dake addabar Mada, Wonaka, Yandoto da Tsafe karkashin jagorancin gawurtaccen shugaban 'yan ta'addan nam, Malam Tukur."

- A cewarsa.

Ya kara da bayyana yadda jami'an 'yan sandan suka cafke mai taimakawa 'yan bindiga da bayanai a Kauran Namoda, Birnin Magaji, Zurmi da karamar hukumar Shinkafi ta jihar.

Kara karanta wannan

Shikenan: 'Yan bindiga sun tare a wani dajin Bauchi, 'yan sanda sun sheke da yawa, sun kawo wasu

Kakakin rundunar ya bayyana yadda suke tsare da wadanda ake zargin, sannan zasu gurfanar dasu gaban kotu da zarar an kammala bincike.

DSS sun cafke kwamandan Boko Haram da yayi wa Buhari maraba a Kogi

A wani labari na daban, jami’an hukumar tsaro ta farin kaya, DSS sun yi ram da kwamandan Boko Haram da ya tada bam ranar da Buhari ya je Kogi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel