Duk Yan Siyasar Da Suka Tunkare Ku da Batun Dabanci Ku Ce Su Kwashi Yaransu, Tambuwal Ga Matasa

Duk Yan Siyasar Da Suka Tunkare Ku da Batun Dabanci Ku Ce Su Kwashi Yaransu, Tambuwal Ga Matasa

  • Gwamna Aminu Tambuwal na jihar Sakkwato ya roki matasa da su guji daban siyasa a yayin zaben 2023
  • Tambuwal ya bukaci matasa da su bukaci yan siyasar da suka yi masu tayin daban siyasa da su yi amfani da yaransu maza da mata
  • Darakta janar na kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na PDP, ya kuma ce Atiku ne zai kawo sauyi a siyasar Najeriya

Sokoto - Gwamnan jihar Sakkwato, Aminu Tambuwal, ya bukaci matasa da su guji bari ayi amfani da su a matsayin yan daban siyasa a yayin zaben 2023.

Tambuwal, darakta-janar na kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), ya bayyana hakan ne a ranar Talata, 3 ga watan Janairu a wajen gangamin yakin neman zaben jam'iyyar a kananan hukumomin Binji da Tangaza.

Kara karanta wannan

An Fallasa Sunan Dan Takarar Shugaban Kasan Da Tinubu Zai Amfani Da Shi Ya Lashe Zaben 2023

Aminu Tambuwal
Duk Yan Siyasar Da Suka Tunkare Ku da Batun Dabanci Ku Ce Su Kwashi Yaransu, Tambuwal Ga Matasa Hoto: Aminu Tambuwal
Asali: Facebook

Duk wanda ya yi maku tayin daban siyasa ku ce ya hada ku da 'ya'yansa, Tambuwal ga matasa

Gwamnan ya shawarci matasa da kada su yarda ayi amfani da su wajen tayar da zaune tsaye da kuma wargaza zaman lafiya da ke nan, jaridar The Cable ta rahoto.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jaridar Daily Post ta nakalto Tambuwal yana cewa:

"Kada ku yarda ayi amfani da ku wajen wargaza zaman lafiya tare da haddasa tashin hankali da hargitsi
"Ku bukaci duk dan siyasar da ya gayyaceku don shiga daban siyasa da ya hada ku da yaransa maza da mata."

Atiku zai kawo sauyi a makomar siyasar Najeriya, Tambuwal

A gefe guda, Aminu Tambuwal ya bayyana cewa Alhaji Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, shine zai kawo sauyi ga makomar siyasar Najeriya idan har ya yi nasarar gaje Shugaban kasa Muhammadu Buhari a zaben 2023.

Kara karanta wannan

Atiku Zai Sauya Rayuwar Yan Najeriya Idan Ya Ci Zabe, Gwwana Tambuwal Ya Yi Magana Mai Jan Hankali

Tambuwal ya kuma jaddada cewar Atiku ya tanadi tsare-tsare na musamman da za su kawo karshen ta'addanci, cin hanci da rashawa da kuma habbaka tattalin arzikin Najeriya.

PDP a rasa wasu manyan jiga-jiganta a jihar Katsina, sun koma APC

A wani labari na daban, mun ji cewa babban jigon PDP a jihar Katsina, Alhaji Sani Abu, ya sauya sheka zuwa APC tare da wasu jiga-jigai da mambobi 1,907.

Tsohon DG na Kamfen Yakubu Lado da sauran yan siyasan sun koma APC a hukumance a yayin da jirgin kamfen din Dikko/Jobe ya dira karamar hukumar Danmusa domin yakin neman zabe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel