'Yan Sandan Bauchi Sun Kashe ’Yan Bindiga da Masu Garkuwa da Mutane a Wata Musayar Wuta
- Rundunar 'yan sandan jihar Bauchi ta yi nasarar hallaka wasu 'yan bindiga da ake zargin suna garkuwa da mutane
- An kama wasu mutum da suka amsa yin garkuwa da mutum hudu tare da karbar kudaden fansa da suka kai N20m
- A bangare guda, an kwato makamai tare da wasu kayayyakin aikata laifuka daga hannun tsagerun 'yan bindigan
Alkaleri, jihar Bauchi - An kashe wasu tsagerun da ake zargin 'yan bindiga ne da masu garkuwa da mutane a wata musayar wuta da suka da 'yan sanda da sauran jami'an tsaro a karamar hukumar Alkaleri ta jihar Bauchi.
An tattaro cewa, an kashe tsagerun ne a lokacin da 'yan sanda da wasu jami'an tsaro suka kai farmaki kan wata mafakar tsageru a Dajin Madam da ke zagayen gidan wasanni da kallon dabbobi na dajin Yankari.
Wasu da yawa daga cikin 'yan bindigan sun tsere da raunukan harbin bindiga, kamar yaadda jaridar Punch ta ruwaito.
Wannan lamari dai ya faru ne a ranar 31 ga watan Disamban 2022, jajiberin sabuwar shekarar da muke ciki yanzu.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, SP Ahmed Wakil ya bayyana cewa, an kwato bindigogin AK-47 guda biyu daga hannun tsagerun a lokacin da suke tserewa.
An kama wasu 'yan bindiga a dajin Yankari
A bangare guda, wata rundunar 'yan sanda mai yaki da masu garkuwa da mutane ta kame wasu masu garkuwa da mutane biyu, Within Nigeria ta tattaro.
A cewar Ahmed, wadanda aka kaman sun amsa cewa, sun yi garkuwa da mutane hudu tare da boye su a dajin Yankari tare da karbar kudin fansa har N20m.
A cewar sanarwar kakakin 'yan sandan, wadanda aka kamen sun hada da Adamu Mohammed mai shekaru 33 da kuma Datti Alh Bula mai shekaru 35 kuma dukkansu 'yan unguwar Mamadi ne a gundumar Pali ta jihar.
Ya zuwa yanzu ya ce ana ci gaba da bincike don gano gaskiya tare da gurfanar dasu a gaban kuliya manta sabo.
An sheke 'yan bindiga hudu a Kaduna
A wani labarin kuma, jami'an tsaro sun yi nasarar hallaka wasu 'yan ta'adda hudu a jihar Kaduna a wani yanayi mai kama da wannan.
An kashe tsagerun 'yan bindigan ne a musayar wuta da sojoji, kamar yadda rahoto ya bayyana a jiya.
Ana ci gaba da samun nasara kan tsagerun 'yan bindiga a Najeriya, musannan ganin yadda suka addabi jama'a.
Asali: Legit.ng