Littafin Pantami Zai Sauya Tunanin Matasa, Gwamna Zulum da Minsita Sirika Sun Siya Kwafi 12,000

Littafin Pantami Zai Sauya Tunanin Matasa, Gwamna Zulum da Minsita Sirika Sun Siya Kwafi 12,000

  • Minista Pantami ya wallafa wani littafin da zai kawo sauyi a tunani da rayuwar matasa masu tasowa
  • An ce littafin ya maida hankali ne wajen shawartar matasa su bi kwarewa sabanin digiri da suka yi
  • Najeriya na fuskantar matsalar zaman banza da rashin aikin yi ga matasa, hakan na ci gaba da jawosabbin matsaloli

Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum da minsitan zirganiyar jiragen sama, Sanata Hadi Sirika sun siya kwafi 12,000 na littafin da minsitan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami ya wallafa.

Littafin mai suna “Skills Rather than Just Degrees” ya yi tsokaci ne ga matasa da su hada sana’ar hannu baya ga karatun digiri da suke don neman hanyar rayuwa a nan gaba, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

2023: Tinubu Ya Daukarwa Al'ummar Arewa Gagarumin Alkawari a Bangaren Almajiranci

A cewar wata sanawar da hadimin Pantami, Femi Adeluyi ya fitar, ya ce shugaban kamfanin fasaha na Microsoft ne ya yiwa littafin rubutun gabatarwa.

Pantami ya wallafa littafi, zai magance matsalar matasa
Littafin Pantami Zai Sauya Tunanin Matasa, Gwamna Zulum da Minsita Sirika Sun Siya Kwafi 12,000 | Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

A cewar sanarwar:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“A kokarin habaka kwarewa ta sana’a a Najeriya, Farfesa Babagana Zulum ya siya kwafi 10,000 na littafin don rabawa a makarantu da sauran cibiyoyi a jihar Borno.
“Sanata Hadi Sirika shima ya siya 2,000 don rabawa cibiyoyin kasar nan.”

Littafin zai magance matsalolin matasa da yawa

Sanarwar ta kuma kara da cewa, littafin na Pantami ya mai da hankali ne ga gano kwarewa da tasirinta ga matasa don rage zaman banza da rashin aikin yi a Najeriya.

Wannan littafin na Pantami dai ya samu karbuwa, domin hukumar jami'o'i ta Najeriya ta bayyana amincewarta ga amfani dashi a jami'o'i da sauran cibiyoyin karatu, kamar yadda jaridar Leadership ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Sojan Fadar Shugaban Kasa Ya Bude Wuta, Ya Yi Sanadiyyar Rasa Rai a Abuja

Hakazalika, manyan farfesoshi kuma shugabannin jami'o'i sun yi bitar littafin tare da bayyana cewa, yana kan turbar da ta dace da halin da kasar nan ke ciki.

Dangote zai samar da ayyuka a Najeriya

A wai labarin kuma, kunji yadda kamfanin Dangote ya kuduri samar da ayyuka a kasar nan, ta hanyar daukar matasa aiki.

Majiya ta bayyana cewa, wannan yunkuri zai kai ga daukar matasa sama da 300,000 aiki a cikin kankanin lokaci.

Daya daga matsalolin matasa a Najeriya shine aikin yi, gwamnatoci da kamfanoni na ci gaba da bayyana daukar mataki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel