Za Mu Magance Matsalolin Almajiranci, Tinubu Ya Baiwa Malaman Arewa Tabbaci

Za Mu Magance Matsalolin Almajiranci, Tinubu Ya Baiwa Malaman Arewa Tabbaci

  • Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya magantu a kan hanyoyin da zai bi don magance kalubalen da ke tattare da Almajiranci a yankin arewacin Najeriya
  • Dan takarar shugaban kasa na APC ya yi alkawarin samar da wata hukuma na musamman da za su yi aiki tare don inganta rayuwar Almajirai da malaman Sangaya
  • Tinubu ya kuma jaddada aniyarsa na ba rayuwar matasa muhimmanci ta yadda za su amfani kansu da kasar

Kano - Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar All Progressive Congress (APC), Bola Tinubu, ya sha alwashin magance matsalolin da ke tattare da tsarin Almajiranci a yankin arewacin Najeriya idan aka zabe shi a matsayin shugaban kasa.

Tinubu ya bayyana hakan ne a ranar alata a Kano yayin wata ganawa da ya yi da shugabannin Musulunci da malamai daga jihohin arewa maso yamma bakwai.

Kara karanta wannan

‘Dan Takaran APC, Tinubu Ya Dage Sai Ya Cire Tallafin Fetur Idan Ya Gaji Buhari

Tsohon gwamnan na jihar Lagas ya ce gwamnatocin baya sun gaza magance matsalar Almajiranci saboda rashin hadin kai da tsare-tsare, Premium Times ta rahoto.

Bola Tinubu
Za Mu Magance Matsalolin Almajiranci, Tinubu Ya Baiwa Malaman Arewa Tabbaci Hoto: @OfficialABAT
Asali: Twitter

Tinubu ya lissafa tangardar da gwamnatin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya samu bayan ya gina makarantun sangaya ba tare da asibitoci da yiwa malamansu tanadi ba.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Zan samar da wata hukuma ta musamman kan Almajiranci, Tinubu

"Bari na amsa tambayar Almajiranci. Ka gina makarantu ba tare da asibitoci ba, yiwa malamansu tanadi, babu alawus.
“Don karfafa tsarin zamantakewar mu da kuma samun tabbass a gaba, saka hannun jari mai yawa a harkar ilimi zai jagoranci matasanmuwajen samun ingantacciyar rayuwa.
“A nan, ina magana ba wai a bangaren abin duniyarsu ba kawai harma da tsarkake zukatansu da rawar ganin da za su taka a matsayinsu na yan kasa masu mutunci.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: 'Yan Bindiga Sun Yi Wa Shugaban Jam'iyyar PDP Yankan Rago a Jihar Arewa

"Kowani da yana da yancin samun ilimi. Ba daidai bane a gansu suna yawo a tituna ko su bar makaranta saboda talauci.
"Idan aka bari na zama shugaban kasa, zan nada wata hukuma ta musamman kuma wannan hukumar da ni kaina za mu yi aiki da ku don samar da mafita mai dorewa a kan kalubalen almajiranci.
"Za mu mayar da matasanmu su zama masu amfani ga kansu da kasar. Su din suna da daraja kuma dole mu dauke su a haka."

Yankin arewa maso yammacin Najeriya na fama da annobar Almajiranci wanda ya haifar da yawan yara marasa zuwa makaranta a yankin.

Ina bukatar goyon bayanku

A wajen taron wanda ya samu halartan mai masaukin baki, Gwamna Abdullahi Ganduje, Tinubu ya ce zai mayar da hankali wajen inganta rayuwar yan Najeriya idan aka zabe shi.

A wani labarin kuma, mun ji cewa wani jigo na jam'iyyar APC a jihar Neja, Musa Ibeto, ya fice daga jam'iyya mai mulki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel