Lafiya uwar jiki: Anfanin rake 9 a jikin dan adam

Lafiya uwar jiki: Anfanin rake 9 a jikin dan adam

Tabbas rake (sugarcane) na da matukar amfani a rayuwar dan adam, sannan yakan kare jiki daga cututtuka da dama,sannan yakan kare garkuwar jikin mutum daga cututtuka bin ciken masana ya inganta amfanin rake ga rayuwar dan adam.

Legit.ng ta zakulo maku kadan daga cikin amfaninsa;

1. Yana kare mutum daga kamuwa da mura da ciwon daji da sanyi.

2. Yana kara ma garkuwar jiki karfi.

3.yana kara ruwan jiki musamman ga masu aikin karfi.

4.yana tema kawa koda wajen sarrafa fitari.

Lafiya uwar jiki: Anfanin rake 9 a jikin dan adam
Lafiya uwar jiki: Anfanin rake 9 a jikin dan adam

KU KARANTA: Illolon shan ruwan sanyi 8 a jikin dan adam

5. Yana kara lafiyar idanu,ciki,hanta da zuciya.

6.yana gyara fata sbd sinadarin Glycolic Acid dake cikinsa.

7.yana kara ma hakora lafiya amman yana da kyau a kuskure baki yayin da aka gama shansa saboda cikin baki akwai bacteria wadan da zasu iya ammafani da wannan zakin su haifar wa da mutum wata cutar misali caris ma'ana tsutsar hakori.

8, baya da illa ga masu ciwon suga amman kada

me type 2 diabetes ya yawai ta shansa.

9. Rake na maganin yunwa da dai sauran muhimman abubuwa.

Da fatan za'ayi ta shan rake.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng