Hawaye Sun Kwaranya Yayin da Tsohon Sanatan PDP Ya Mutu a Asibitin Abuja

Hawaye Sun Kwaranya Yayin da Tsohon Sanatan PDP Ya Mutu a Asibitin Abuja

  • Jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta rasa daya daga cikin manyan jiga-jiganta a Bayelsa, Inatimi Spiff
  • Spiff, tsohon sanata wanda ya wakilci yankin Bayelsa ta Gabas, ya mutu a ranar Asabar, 24 ga watan Disamba, a asibitin Abuja bayan dan gajeruwar rashin lafiya
  • PDP ta yi alhinin mutuwar dan siyasan, tana mai cewa yana ta aiki don ganin Atiku ya yi nasara a 2023 kafin Allah ya karbi ransa

Bayelsa - Allah ya yiwa tsohon sanata wanda ya wakilci Bayelsa ta Gabas a majalisar dokokin tarayya, Inatimi Spiff, kamar yadda jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta bayyana a wata sanarwa da ta fitar.

Shahararren dan siyasan wanda ya fito daga Twon-Brass a karanar hukumar Brass ta jihar Bayelsa ya rasu ne a ranar Asabar, 24 ga watan Disamba, a asibitin Abuja bayan yar gajeruwar rashin lafiya, PM News ta rahoto.

Kara karanta wannan

Da Dumi-ɗumi: Hadimin Gwamnan Jam'iyyar APC Ya Mutu a Hatsarin Mota

Inatimi Spiff
Hawaye Sun Kwaranya Yayin da Tsohon Sanatan PDP Ya Mutu a Asibitin Abuja Hoto: Dogitimiye Sam, Williams Faith
Asali: Facebook

Legit.ng ta tattaro cewa kakakin PDP a jihar Bayelsa, Ebiye Egoli, ya sanar da labarin mutuwar tsohon sakataren gwamnatin jihar a tsohuwar jihar Ribas a ranar Litinin, 26 ga watan Disamba.

Jawabin na cewa:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Cike da nauyin zuciya da bakin ciki muka samu labarin mutuwar shugabanmu, uba, aboki, dan uwa kuma daya daga cikin ginshikan PDP a jihar Bayelsa, Mai girma Sanata Inatimi Rufus Spiff wanda aka gaggauta kaiwa asibiti a Abuja bayan ya kamu da rashin lafiya.
"Amma abun bakin ciki a cewar majiyoyin iyalin, bai tashi ba ya amsa kiran Allah."

Wani rahoton Daily Independent ya bayyana cewa tsohon sanatan ya rasu yana da shekaru 68 a duniya.

PDP ta mika ta'aziyya ga iyalin

Jam'iyyar PDP reshen jihar Bayelsa ta ce mutuwar Sanata Spiff ya jefa jam'iyyar cikin bakin ciki da alhini.

Kara karanta wannan

Dan Sanda Ya Harbe Wata Lauya a Hanyarta Ta Dawowa Daga Coci a Ranar Kirsimeti

Ta kara da cewar marigayin ya nuna cikakken goyon bayansa ga takarar shugabancin Alhaji Atiku Abubakar da abokin takararsa, Gwamna Ifeanyi Okowa.

Jam'iyyar ta ce:

"Zuciyarmu na tare da iyalan mamacin kuma muna addu'an Allah madaukakin sarki ya basu karfi da juriyar daukar wannan babban rashi da mutuwarsa zai haddasa.
"Allah ya ji kan shugabanmu, Marigayi Sanata Inatimi Rufus Spiff da ya rigamu gidan gaskiya, Ameen."

Hadimin Gwamnan Jihar Ebonyi ya mutu a hatsarin mota

A wani labarin, mun ji cewa Allah ya yiwa hadimin gwamna David Umahi na jihar Ebonyi, Mista Sunday Agwu, rasuwa sanadiyar hatsarin mota.

Asali: Legit.ng

Online view pixel