Kotu Ta Yankewa Akanta Daurin Shekaru 304 a Sakamakon Kama Shi da Laifin Sata

Kotu Ta Yankewa Akanta Daurin Shekaru 304 a Sakamakon Kama Shi da Laifin Sata

  • Babban kotun jiha da ke garin Enugu ta samu Emmanuel Sombo da laifin satar kudin FCE Eha-Amufu
  • Emmanuel Sombo ya yi amfani da sa-hannun shugabannin makarantarsa, ya cire N34m daga banki
  • Bayan ya karbo kudin daga banki, Alkali ya tabbatar da cewa Akantan ya yi abin da ya ga dama da su

Enugu - Wata babban kotu da ke zama a jihar Enugu, ta yanke hukuncin daurin shekaru 304 ga Mista Emmanuel Sombo a dalilin laifin satar kudi.

Rahoton da muka samu daga Vanguard a ranar Talata, ya nuna cewa Alkali Kenneth Okpe ya samu Emmanuel Sombo da laifin da EFCC take tuhumarsa.

Ana zargin Mista Sombo ya yi amfani da takardu ya saci N34.9m daga asusun kwalejin koyar da ilmi ta tarayya da ke Eha-Amufu a jihar Enugu.

Kara karanta wannan

Borno: Boko Haram Sun Kai Hari, Sun Kone Gidaje 7, Kayan Abinci da Dabbobin Jama’a

Wanda ake tuhuma shi ne Akanta a wannan makaranta, tun shekarar 2010 yake shari’ar da hukumar EFCC a wata kara mai lamba E/56C/2010 a kotu.

Sa hannun bogi ko hada-kai?

Ana zargin Akantan ya yi irin sa hannun shugabannin makarantar tarayyar domin cire kudi daga asusunsu da ke wani banki domin yin hidimar gabansa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Shugabannin kwalejin a lokacin wanda suka hada da Shugaba, Magatakarda da Mai kula da kudi duk musanya sa hannu a kan takardun cire kudi a bankin.

Gidan yari
Gidan yari a Najeriya Hoto: Getty Imahes
Asali: Getty Images

Jaridar Sun ta rahoto Mai shari’a Kenneth Okpe ya ce ya gamsu cewa Emmanuel Sombo ya yi amfani da sa hannun ma’aikatan, ya cire kudi da sunansu.

Alkalin ya ce kotu ta karbi hujjojin da masu shigar da kara suka bada, don haka ya kama wanda ake zargi da duk jerin laifuffukan da EFCC take zarginsa.

Kara karanta wannan

Kotu Ta Yanke Wa Matashi Ɗan Shekara 20 Ɗaurin Gidan Yari A Jihar Arewa Saboda Lalata Allunan Kamfen Ɗin Atiku

Sata ta tabbata inji Alkali

"Duk wasu shika-shikan sata sun bayyana a shari’ar nan. Wanda ake tuhuma ya fadawa EFCC cewa ya san takardun cire kudin na bogi ne…
Amma ya ce mai gidansa ne ya umarce shi da ya yi duk abubuwan da ake bukata.
Ya yi amfani da takardun, ya cire kudi daga banki, a karshe ya hana kwalejin horar da ilmin na Eha-Amufu damar mallakar kudin."

- Kenneth Okpe

Hakan ya sa Alkali ya daure Sombo na shekaru uku a kan kowane laifi da ya aikata daga zargi na 32 zuwa 61, ya ce wa’adin za suyi aiki ne duk a tare.

Shinkafa ta gagari Gwamnati

An ji labari buhun shinkafa ya yi tsada sosai a kasuwa, hakan ya sa ya Gwamnan jihar Anambra ya soke rabon shinkafar kirismeti a shekarar nan.

A madadin haka, an yi karin albashi, sannan Gwamnatin Chukwuma Charles Soludo za ta ba duk wani ma’aikaci N15, 000 domin ya yi shagalin kirismeti.

Kara karanta wannan

Zabe ya karaso, Hukumar INEC ta Jero Manyan Abubuwa 2 da take Tsoro a 2023

Asali: Legit.ng

Online view pixel