Boko Haram Sun Kutsa Yankunan Borno, Sun Kone Gidaje, Kayan Abinci da Dabbobi

Boko Haram Sun Kutsa Yankunan Borno, Sun Kone Gidaje, Kayan Abinci da Dabbobi

  • Miyagun ‘yan ta’adda da ake zargin na Boko Haram/ISWAP ne sun kai farmaki yankunan Jibwiwi dake karamar hukumar Hawul ta jihar Borno
  • An gano cewa ba su halaka ko mutum daya ba amma sun kone gidaje bakwai tare da daruruwan buhunan masara, gero, dawa da gyada sai dabbobi
  • Tuni mafarauta suka hanzarta bin su amma basu same su ba sai a Ngulde dake karamar hukumar Askira Uba inda suka tsere cikin dajin Sambisa

Borno - ‘Yan ta’adda da ake zargin mayakan Boko Haram ne da ISWAP a yammacin Litinin sun kutsa yankunan Jibwiwi dake karamar hukumar Hawul ta jihar Borno inda suka bakawa gidaje bakwai wuta da daruruwan buhunan masara, gero, dawa, gyada da wasu dabbobi.

Taswirar Borno
Boko Haram Sun Kutsa Yankunan Borno, Sun Kone Gidaje, Kayan Abinci da Dabbobi. Hoto daga TheCable.ng
Asali: UGC

Wannan na zuwa ne bayan jami’an tsaro sun karba sama da mutum 80,000 da suka tuba daga ta’addanci a kungiyar.

Kara karanta wannan

Abin takaici: An yi jana'izar wasu ma'aurata da 'yan bindiga suka kashe bayan karbe kudin fansa N7.5m

Duk da Vanguard ta tabbatar da cewa babu ran da aka rasa, ‘yan ta’addan da suka bayyana a babura masu tarin yawa dauke da bindigogi AK47 da bama-baman fetur sun shiga Jibwiwi wurin karfe 6 na yamma inda suka ci karensu babu babbaka.

Sakamakon abinda ya faru, shugaban kungiyar mafarauta dake yankin arewa masu gabas wanda ya fito daga karamar hukumar Hawul, Mohammed Shawulu Yohanna ya gaggauta tura tawagarsa zuwa yankin don ceto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Cike da takaici, tawagar ceton ta isa Jibwiwi, yayin da ‘yan ta’addan suka riga da suka tsere tare da shiga yankin Ngulde dake karamar hukumar Askira Uba.

Cike da sa’a, yayin da ‘yan ta’addan suka hango ababen hawan mafarautan karkashin shugabancin Yohanna, sun janye tare da tserewa cikin dajin Sambisa.

A yayin zantawa da jaridar Vanguard kan wannan cigaban, shugaban mafarautan arewa maso gabas yace:

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Jama'a suna ta mutuwa bayan cin abinci mai guba a wata karamar hukuma

“Na samu kiran gaggawa kan cewa wasu ‘yan ta’adda sun kutsa Jibwiwi, da gaggawa na aike tawagata zuwa wurin amma yayin da suka isa Jibwiwi, ‘yan ta’addan sun tsere bayan barnar da suka yi.
“Sun yi nasarar kone gidaje bakwai da buhunan shinkafa, masara, gyada, gero da wasu kayan abinci da jama’a suka girbe tare da dabbobi.
“Daga nan mun fatattake su zuwa Ngulde, amma yayin da suka kutsa, sun yi nasarar aiwatar da mugun nufinsu. Bayan ganinmu sun tsere zuwa dajin Sambisa.”

- Yohanna wanda ya bayyana bidiyon farmakin ya sanar da Vanguard.

’Yan bindiga sun rufe babbar hanyar Gusau zuwa Dansadau

A wani labari na daban, miyagun ‘yan bindiga sun kai farmaki an matafiya a hanyar Gusau zuwa Dansadau dake jihar Zamfara.

An gano cewa harin daukar fansa suka kai bayan halaka wasu 15 da aka yi a Maigoge bayan sun farmaki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel