Minista Ta Gagara Rike Hawaye, Ta Fashe da Kuka Kan ‘Yan Matan da B/Haram Suka Dauke

Minista Ta Gagara Rike Hawaye, Ta Fashe da Kuka Kan ‘Yan Matan da B/Haram Suka Dauke

  • Ministar harkokin mata a Najeriya ta zubar da hawaye da aka yi mata tambaya a kan halin Leah Sharibu
  • An yi shekaru hudu da ‘Yan Boko Haram suka dauke Leah Sharibu, har yanzu ba a san yadda take ciki ba
  • Paulen Tallen ta yi bayanin yadda Gwamnatin Muhammadu Buhari take kokarin ceto yaran da aka dauke

Abuja - Ministar harkokin mata, Paulen Tallen ta gaza tsaida hawaye yayin da ta tuna da ‘yan matan da ‘yan ta’adda suke cigaba da tsare su.

The Guardian ta ce Paulen Tallen tayi kuka a lokacin da ake daukar taro kai-tsaye domin nuna irin nasarorin da gwamnatin APC mai-ci ta samu.

Ministar matan ta dauki lokaci tana gabatar da bayanin kokarin da ma’aikatarta tayi tsakanin 2015 da 2013 a wannan taro wanda shi ne karo na 13.

Kara karanta wannan

Abin takaici: An yi jana'izar wasu ma'aurata da 'yan bindiga suka kashe bayan karbe kudin fansa N7.5m

Gidan talabijin NTA da gidajen rediyon Najeriya da Voice of Nigeria sun dauki shirin kai-tsaye.

Leah Sharibu: Kokarin da muke yi - Minista

A wajen wannan shiri sai aka bijirowa Mai girma Ministar da batun Leah Sharibu – wata ‘yar makarantar da ‘yan ta’addan Boko Haram suka dauke.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A cewar Ministar tarayya, idan aka shiga ofishinta, za a ga hotunan yadda ta ziyarci iyayen Sharibu, kuma ta zauna da su, ta kwantar masu da hankali.

Ministar mata
Paul Tallen a Aso Rock Hoto: naijanews.com
Asali: UGC

Tsohuwar mataimakiyar gwamnar ta ce duk takardar da ta kai wa Shugaban kasa kan abin da ya shafe ta, ya na amincewa ba tare da bata lokaci ba.

Tallen tace bayan zuwa garin Chibok da tayi sau uku, sojoji sun ba ta jirgin sama, ta hadu da iyayen yarinyar a garin Yola saboda rashin tsaro a Borno.

Kara karanta wannan

Tsohuwar Abokiyar Gabar Bola Tinubu Ta Bayyana Halin Lafiyar ‘Dan Takaran APC

Gwamnati ta na bakin kokari

Jaridar Vanguard ta rahoto Hon. Tallen tana cewa shugaba Muhammadu Buhari ya damu da halin da yaran da aka dauke suke ciki, ana kokarin ceto su.

Sha’anin tsaro aikin kowa ne, saboda haka sai kowa ya bada gudumuwarsa da ya lura da wani abu.

Ina addu’a Ubangiji ya kawo ranar da ‘Yan Najeriya za su rika ba jami’an tsaronmu bayanan da suka dace domin a gano wadannan ‘yan mata.

Ministar ta ce kullum ta na masu addu’a, daga nan ta fashe da kuka, tana cewa yanzu lokaci ne da za a nuna kauna ga wadanda ke hannun miyagun.

Ina Leah Sharibu?

A shekarar 2018 Boko Haram suka shiga wata makaranta, suka sace Leah Sharibu tare da wasu yara 109, har zuwa yanzu yarinyar tana hannunsu.

Duk da an saki sauran abokan karatunta, budurwar tana tsare a sakamakon kin musulunta da tayi, Ministar tayi hawaye da ta tuna da ita a yau.

Kara karanta wannan

Majilissar Dokokin Kasa A Nigeria ta Ce Babban bankin Kasa Ya Tsaya Da Batun Cire Kudi Tukunna

A 2019, an rahoto Ministan yada labarai da al'adu, Lai Mohammed ya ce Leah Sharibu tana nan da ran ta, ya ce 'yan adawa ke yada jita-jitar mutuwarta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel