Hukuncin Abduljabbar Kabara: Maganganun Maqary, R/Lemu da wasu Malaman Musulunci

Hukuncin Abduljabbar Kabara: Maganganun Maqary, R/Lemu da wasu Malaman Musulunci

  • Malamai sun tofa albarkacin bakinsu a kan hukuncin da aka zartar a kan Abduljabbar Nasiru Kabara
  • Alkalin kotun shari’a ya yanke hukuncin kisan-kai a dalilin batanci ga Annabi SAW ga shehin malamin
  • Malamai da-dama sun yaba da hukuncin da kotun shari’a ta yi wa Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara

Kano - A ranar Alhamis, 15 ga watan Disamba 2022, kotun shari’a ta yanke hukuncin kisa ga malamin addinin nan, Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara.

A wannan rahoto, Legit.ng Hausa ta tattaro abin da wasu daga cikin malaman musulunci suke fada kan hukunci da Ibrahim Sarki Yola ya zartar.

Dr. Ibrahim Disina, shahararren malamin addinin Musulunci a garin Bauchi, yana cikin wadanda suka fara yada labarin, amma bai ce komai ba a kai.

Shi Dr. Kabir Asgar a rubutun da ya yi a Facebook, ya yi godiya ga gwamnatin Kano, kotun shari’a, malaman addini, da daukacin al'ummar musulmai.

Kara karanta wannan

Babban Jigon APC Kuma Tsohon Shugaban Majalisar Dokoki Ya Rasa 'Ya'Yansa Biyu a Hatsari

Malamin yake cewa Alƙalin da ya yanke hukunci ya farantawa al'umma rai. A karshe ya ce Allah (SWT) ya sa a samu ƙarfin gwiwar zartar da kisan.

Abubuwan A Fili Suke - Rabi'u Rijiyar Lemo

Muhammad Rabi'u Rijiyar Lemo ya yi tsokaci a kan shari’ar, ya ce tun farko Abduljabbar Nasiru Kabara ya yi kalaman batanci a kan Manzon Allah.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A cewar Dr. Muhammad Rabi'u Rijiyar Lemo, malamin ya gagara nuna inda lafazin ya zo a littafan musulunci, a karshe yake cewa gaskiya ce tayi halinta.

Abduljabbar Kabara
Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara Hoto: www.dw.com / Aliyu Samba
Asali: UGC
"Mutum ne ya yi kalaman Batanci ga Manzon Allah S.A.W kuma ya ce, wadannan kalaman suna cikin littattafan malaman Musulunci, ya ma ayyana sunayen wadannan littattafai, tare da juzu'i da shafi. Aka nemi ya buda wadannan littattafai ya nuna inda wadannan kalamai suke amma ya gaza, sai ya koma kame-kame da cewa ai shi da ma'ana yake riwaya. Ita ma ma'anar aka ce nuna lafazin da ya zo da wannan ma'anar shi ma hakan ya gagara.

Kara karanta wannan

Kano: Abubuwan da ya Dace Ku Sani Game da Sheikh Abduljabbar Kabara

Alhamdu lillahi, yau gaskiya ta kara bayyana."

- Muhammad Rabi'u Rijiyar Lemo

Ranar farin ciki ga Muminai

Farfesa Mansur Ibrahim Sokoto, malamin hadisi a Sokoto, ya ce jiya rana ce ta farin ciki ga muminai saboda an kare kimar Annabi SAW da sahabansa.

"Rana ce da muminai suke murna da taimakon Allah'. Allah mun gode maka. Ka kara kare martabar manzonka da iyalansa da almajiransa da masoyansa har ranar tashin alkiyama. Ka tozarta, tare da wulakanta duk mai keta alfarmarsu.

Alhamdu lillah"

- Farfesa Mansur Ibrahim Sokoto

Shi kuwa Farfesa Ibrahim Maqari ya sha bam-bam, yana ganin banbamcin siyasa ya jawo aka zartar da wannan hukunci a kan Sheikh Kabara ba komai ba.

Ibrahim Maqari ya ce a tarihi, mafi yawan wadanda aka kashe da sunan zindiƙancin, ba shi ne asalin laifinsu ba, illa iyaka ana fakewa da wannan ne kurum.

“Mafi yawan waɗanda aka kashe saboda tuhumar zindiƙanci a tarihi idan mai karatu ya zurfafa bincike zai samu rikicin siyasa ne ya haɗasu da masu mulki…Amma ba zindiƙancin ne dalilin kisan ba.”

Kara karanta wannan

Bidiyon Yadda Aka Yi Dirama a Zaman Yanke Wa Sheikh Abduljabbar Hukunci da Cikakken Jawabinsa Na Karshe

- Farfesa Ibrahim Maqari

Muhammad Sani Umar Rjiyar Lemo ya jawo wata aya daga Suratul Hjjr a shafinsa na Facebook.

Wannan aya ta Al-Kur’ani tana nuna Allah madaukakin Sarki (SWT) zai kare Annabi Muhammad (SAW) daga izgilancin duk wasu masu yi masa izigili.

Za a rataye Abduljabbar Kabara

A ranar Alhamis ne aka samu rahoto cewa Alkali ya yanke hukuncin kisan kai a kan Sheikh AbdulJabbar Nasiru Kabara bisa samun shi da laifin batanci.

Gwamnatin jihar Kano ta gurfanar da Malamin gaban kotun shari'a da laifin cin mutuncin Manzon Allah SAW, a karshe jiya Alkali ya same shi da laifi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng