Abubuwan da Suka Dace a Sani Game da Abduljabbad Kabara, Wanda Yayi Batanci ga Annabi

Abubuwan da Suka Dace a Sani Game da Abduljabbad Kabara, Wanda Yayi Batanci ga Annabi

  • Kotu ta yankewa Abduljabbar Nasiru Kabara, malamin addinin musuluncin nan da ya dade yana jawo cece-kuce, hukuncin kisa ta hanyar rataya
  • Hakan ya biyo bayan tabbatar da laifin batanci ga fiyayyen halitta da yayi har sau tara a wa'azozinsa da furuci ga al'umma
  • Hakan ya tilasta malaman addini kai kararsa gwamnatin jihar Kano, don gudun rikici da zubda jinanai a al'ummar musulmai

Kano - Babbar kotun shari'a ta Kano ta yankewa Malamin addinin musuluncin nan mazaunin jihar Kano da ya dade yana jawo cece-kuce, Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara hukuncin kisa ta hanyar rataya.

Hakan ya biyo bayan kotun ta yankewa malamin addinin da ya dade yana jawo rikici hukunci bayan kamasa da laifin batanci ga fiyayyen halitta, Annabi Muhammadu S.A.W.

Abduljabbar Kabara
Abubuwan da Suka Dace a Sani Game da Abduljabbad Kabara, Wanda Yayi Batanci ga Annabi. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Daily Trust ta tattaro wasu daga cikin abubuwan da ya kamata ku sani game da malamin.

Kara karanta wannan

Bidiyon Yadda Aka Yi Dirama a Zaman Yanke Wa Sheikh Abduljabbar Hukunci da Cikakken Jawabinsa Na Karshe

  • Abduljabbar Nasiru Kabara malami ne mai shekaru 52, kuma sanannan malamin Kadiriyya ne a jihar Kano, Najeriya, wanda aka zarga da batanci ga fiyayyen halitta (SAW)
  • Shi 'da ne ga Sheikh Nasiru Kabara, tsohon shugaban Kadiriyya na yankin yammacin Afirka, kuma kani ne ga Karibullah Nasiru Kabara, magajin marigayin mahaifinsu.
  • Abduljabbar yayi fice, a matsayin mabiyin darika da Sunna a al'ummar musulman Najeriya, wanda ke koyi da mahaifinsa.
  • Sai dai, a shekarar 2020, yayin zantawa da BBC, ya bayyana yadda ya shiga Shi'a.
  • An sha zargin Abduljabbar da laifin batanci ga fiyayyen halitta Annabi Muhammad (SAW) da wasu daga cikin sahabbansa a wa'azinsa da furuci a cikin al'umma.
  • An yi nasarar cafke Abduljabbar ne bayan malaman addinin Islama na jihar Kano daga Izala, Salafiyya, Tijjaniyya da Kadiriyya sun kai kararsa wajen gwamnatin jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Da walakin: Ra'ayoyin jama'a game da hukuncin da aka yankewa Sheikh Abduljabar

A cewarsu:

"Sun ci karo da lafinka tara na batanci ga annabi Muhammad da Abduljabbar yayi a wa'azozinsa a bidiyo da na murya, wadanda za su zama hujja cewa Abduljabbar na batanci ga fiyayyen halitta, wanda idan ba a kula ba, sabon zai yi sanadiyyar zubda jinanai da rikici a cikin jihar."

Gwamnati ta shirya mukabala

Gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin Abdullahi Umar Ganduje ta yanke shawarar shiga lamarin ta hanyar shirya mukabala tsakanin Abduljabbar da wadanda suke zarginsa, don ya gabatar da hujjojinsa a kan abun da yayi wa'azi a kai.

A ranar 10 ga watan Yuli, gwamnatin jihar Kano ta shirya mukabalar tsakaninsa da sauran malamai hudu dake wakiltar Izala, Salafiyya, Tijjaniyya da Kadiriyya.

Abduljabbar bai amsa tambayoyi ba

Bayan kammala mukabalar da Farfesa Salisu Shehu daga jami'ar Bayero ya shirya kuma ma'aikatar kula da lamurran addini ta Kano ta kula da shi, shugaban mukabalar, ya bayyana cewa Abduljabbar bai amsa ko daya daga cikin tambayoyin da sauran malaman suka yi masa ba.

Kara karanta wannan

Bidiyon Shugaban Kasan South Sudan Yana Fitsari A Wando Ana Tsakiyar Taro

A cewarsa:

"Abduljabbar yayi ta kauce tambayoyin ta hanya bada dalilai marasa amfani ko ya ce babu isashshen lokacin da za'a kawo hujjoji daga littafai sama da dari biyar da yazo dasu wajen mukabala, duk da yana da hadimai, yayin da sauran malaman suka bada hujjohlji da amsoshi ga Abduljabbar kai tsaye."

A ranar 17 ga watan Yuli, 2021, an tsare Abduljabbar bisa zargin da ba a gama yanke masu hukunci a kan batanci ga fiyayyen halitta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel