Muhimman Abubuwan Da Suka Faru A Zaman Yankewa Abdul-Jabbar Hukunci
- Hukunci hudu kotu ta yankewa Abdul-Jabbar, uku daga cikin hukuncin na gwamnatin jihar kano ne, yayin da kuma daya hukuncin na Abdul-Jabbar ne
- Mutane a fadin Najeriya sun tofa albarkatun bakinsu kan wannan hukunci da aka yanke
Kano: Yau 15 ga watan Disambar shekarar 2022, itace ta kawo karshen shari'ar da ake yi wa shararren malamin addinin musuluncin nan, Sheik Abdul-Jabbar Nasiru Kabara inda ta same shi da laifi tare da yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya.
Mai Ya Faru Har Aka Yanke Hukuncin
Mallam Abddul-Jabbar ya fara gabatar da wasu karattuka wanda suka sabawa yadda malamai ke karantarwa, ta fannin usulubin karatun, fassararsa hadi da tarjamar gundarin abubuwan da malamai ko mutane suka sani tun asali.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Misali a bangaren karatun hadisan Manzon Allah S.A.W, Abdul-Jabbar na ganin wasu abubuwan jingina masa akai, bai yi su ba ko kuma bai umarni da ayisu ba.
Hakan Yasa wasu malamai daga ciki da wajen jihar kano suka fara maida masa da martani da kuma nuna masa abinda yake yi bai dace ba kuma kuskure yake aikatawa. Amma duk da haka Abdul-Jabbar din ya hakimce cewa shi akan dai-dai yake.
Mallam Abdul-Jabbar ya nemi da gwamnatin jihar Kano ta hada masa zama da wadannann malaman da suke ganin fahimtarsa ba dai-dai bace. Inda aka jiyo shi a wani faifen bidiyo yana cewa:
"Duk malamin da ya kuma cewa Abul-Jabbar kaza, gwamnati ki hada min zama da shi, in ya kasa kare kansa ko na kasa a daureshi life in prison" inji Abdul-Jabbar din
Anyi Zaman
Kamar Yadda legit.ng Hausa ta rawaito a ranar 10 ga watan yunin shekarar da ta gabata an gudanar da zaman a ma'aikatar shari'a da kula da al'amuran addini ta jihar Kano, karkashin jagorancin kwamishinan ma'aikatar Muhammad Tahir Baba impossible.
Malamai Hudu dai sune suka kalubalanci mallam Abdul-Jabbar daga bangarori hudu na mibiya addinin musulunci a jihar kano, wanda suka hada da Qadiriyya, Tijjaniyya, Salafiyya Da Kuma Izala.
A karshen Zaman, alakalin musabaqar Prof. Salisu Shehu wanda yake shugaban jami'ar Al-Istiqama dake kano, ya sanar da cewa da'awar da Mallam Abdul-Jabbar yakeyi ba gaskiya bane kuma ya kasa kare wasu maganganu da yake yi a karatunsa dan haka gwamnati ta dau mataki a kansa.
Kaishi Kotu
Bayan zaman da akayi a ranar 10 ga watan Yulin 2021, a ranar 14 ga watan Yuli, Mallam Abdul-Jabbar ya fitar da wasu kasusuwa da yake zargin ba'ai masa adalici ba a wajen muqabalar da aka shirya.
A ranar 17 ga watan Yulin dai, gwamnatin kano ta bada umarnin a kama Abdul-Jabbar tare da kaishi kotu, sai dai kuma kotun ta turashi gidan dan kande kafin fara sauarara karar.
Tun daga wannan lokaci aka fara gudanar da shari'ar har zuwa yau din nan 15/12/22 da aka yanke masa hukunci.
Mallam Awaisu Al'arabiy fagge wani wanda yake sa ido a sha'annin shari'ar yace zaman ya gudana ne sau ashirin da tara. Amma yace akwai wani wanda azo zaman kowa ya gufarna amma alkali bai samu damar halartar kotun ba, dan haka ba'ai ba, in kuma har shi to talatin kenan inji Awaisu.
Yanke hukunci
A yau zaman ya kasance na musamman, sabida a yaune aka zo karshen wannan shari'ar kuma a yaune aka gamata gaba dayanta.
Mai shari'a alkali Ibrahim Sarki Yola shine wanda ya jagoranci shari'ar wadda aka fara da misalin karfe 9:17 na safe kuma aka gama ta da misalin karfe 1:23 na yamma a kotun kofar Kudu, dake kudu da fadar Mai-martaba sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero Cfr.
Mai shari'a yace ana tuhumar wanda ke gabana da laifuka guda hudu, wanda suka hada da; Keta Alfarmar Musunci da Manzo S.A.W, Yin wa'azin da zai tada tarzoma, Cin zarafin alkali da kotu da kuma laifukan da suka sabawa al'ummar da muke ciki.
Alkalin ya bawa Abdul-Jabbar damar gabatar da wata magana kafin yanke hukunci, sai dai Abdul-Jabbar din yace ayi masa duk abinda za'ai masa, kuma duk abinda alkali ya fada sharri ake masa.
Bayan jin ta bakin mallam Abdul-Jabbar, sai mai shari'a ya tafi hutun rabin lokaci, bayan mintuna 35 sai ya dawo kuma ya karanto hukunci kamar haka:
Hukunci
"Ni mai shari'a Ibrahim Sarki Yola Alkalin kotun musulunci da ke zamanta a kofar Kudu, na samu wanda ake zargi da laifin da ake zarginsa akai, dan haka ina mai sanar da hukunci: Kotu ta yankewa wannan Mutumi hukuncin kisa ta hanyar rataya, sannan tai umarni da a rufe masallatansa guda biyu na Filin Mushe dake karamar hukumar Gwale, da kuma na sabuwar Gandu. Sannan in Mai bada umarni ga duk gidajen radiyon da suke kano, da kuma gidajen talabijin, da kafafen sadarwa na zamani da su daina sanya karatuttukansa, sannan duk littafan da yazo da su kotu yake karantawa dan bada sheda na kwace su"
Mai shari'a bai gushe ba sai da yace kana da damar daukaka kara daga nan zuwa kwana talatin kan wannan hukuncin.
Abubuwan Da Suka Faru Bayan Zaman Kotun
Bayan zaman kotun jami'an hukumar kula da gyaran hali na Nigeria sun tisa keyar mallam din zuwa gidan yarin Gwaron Dutse, da ke da tazarar kilomita tara daga kotun.
Mutane da dama sun bayyana ra'ayoyinsu kan wannan batu tare da nuna goyan baya ko akasin haka kan wannan hukuncin, kamar yadda legit.ng Hausa ta tattaro
Asali: Legit.ng