Kotu Ta Sanar Da Ranar Da Zata Yankewa Mallam Abdul-Jabbar Hukunci

Kotu Ta Sanar Da Ranar Da Zata Yankewa Mallam Abdul-Jabbar Hukunci

  • Gwamnatin jihar Kano ta zargi Mallam Abdul-Jabbar da yin wa'azin da zai'iya tada tarzoma a jihar kano
  • A karshen shekarar da ta gabata ne, gwamnatin Kano ta shirya wata muhawara wadda ta hadata tsakanin malaman kungiyoyin addinin jihar kano da shi Mallam Abdul-Jabbar din
  • Alkalin muhawarar Prof. Salisu Shehu ya tabbatawar da gwamnati cewa duk da'awar da Mallam Abdul-Jabbar yakeyi ta sabawa ka'ida kuma ya kasa kare ta, dan haka yake sanar da gwamnatin ta dau mataki. Hakan yasa gwamnatin ta maka shi a gaban kuliya

Kano: Kotun shari'ar musulunci dake birnin Kano a arewacin Nigeria ta saka ranar 15 ga watan Disamba 2022 don yanke hukunci kan tuhume-tuhumen da da ake yi wa malamin nan Sheik Abdul-Jabbar Nasiru Kabara.

Gwamnatin Kano na tuhumar shehin malamin da yin batanci ga Annabi Muhhamad S.A.W kuma aka tsare shi tun watan Yulin bara. Rahoton BBC Hausa

Kara karanta wannan

ICPC Ta Kama Wani Jami'in Rundunar Tsaro Ta NSCDC Da Zamba Cikin Aminci

Abduljabbbar zai sake bayyana a gaban mai shari'a Ibrahim Sarki Yola na kotun da ke kofar kudu ne sabida yadda doka ta tanadar duk mai samun fiye da N30,000 duk wata lauyoyin gwamnati baza su tsaya masa ba.

Abdul-Jabbar
Kotu Ta Sanar Da Ranar Da Zata Yankewa Mallam Abdul-Jabbar Hukunci Hoto: BBC Hausa
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kafin tsare Mallamin yayi ikirarin cewa yana kare janibin Manzon Allah S.A.W yake yi, ba kamar yadda ake zarginsa da yi.

Hakan yasa gwamnati ta shhirya masa muhawara da malaman kano, wanda daga baya alkalin muhawarar ya sanar da Abdul-Jabbar ya gaza kare ikirarinsa.

Mallam Abdul-Jabbar ya kasance 'da ne ga shararren malamin Qadiriyyyar nan na yamancin Afrika wata Nasiru Kabara.

Wadanne Malamai Ne Sukai Muhamwara Da Abdul-Jabbar?

Jaridar Manhaja ta Blue Print, ta rawaito jerin malaman da sukai muhawara da malamin a jihar kano. Malaman sun hada da:

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari Ta Ceto ‘Yan Najeriya Daga Yunwa Inji Ministan Buhari

Mallam Rabi'u Umar Rijiyar Lemo shine wanda ya wakilici kungiyar Izala ta jihar kano yayin muhawarar da Abdul-Jabbar.

Mallam Kabir Abdul-Hamid wanda akewa laqabi da hayiqi fidda na kogo shi ne ya wakilci 'bangaren Salafiyya.

Mallam Ma'ud Hotoro ne shine wanda ya wakilci 'bangaren malamin wato Qadiriyya. kuma ba da jimawa da yin muhawarar ba Allah ya karbi ransa.

Daga 'bangaren Tijanniya kwa Mallam Abubakar Madatai shi ne ya wakilcesu tare da sukar da'awar tasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel