"Me Ya Hada INEC Da Yin Taron Siyasa A Coci": MURIC Ta Soki Hukumar INEC Ta Legas Kan Shirya Taro A Coci

"Me Ya Hada INEC Da Yin Taron Siyasa A Coci": MURIC Ta Soki Hukumar INEC Ta Legas Kan Shirya Taro A Coci

  • Farfesa Ishaq Akintola, shugaban kungiyar kare hakkin musulmi, MURIC, ya soki shirya yin taron siyasa da INEC ta Legas ta shirya yi a wani coci da ke Ikeja
  • Akintola ya ce wannan matakin abin zargi ne duba da yadda cocin ta ke nuna ra'ayinta a harkokin siyasa a fili sannan a dauki taron siyasa a kai coci
  • Shugaban na kungiyar musuluncin ya yi kira da hukumar INEC ta kasa da ke Abuja ta ja kunnen INEC ta Legas ta dena yin tarukan siyasa a wuraren ibada tunda akwai wasu wuraren daban

Kungiyar kare hakkin musulmi a Najeriya, MURIC, ta soki hukumar zabe mai zaman kanta INEC reshen jihar Legas saboda shirya taronta cikin coci a Ikeja, jihar Legas.

Shugaban na MURIC, Farfesa Ishaq Akintola, ya yi wannan sukar cikin sanarwa da kungiyar ta fitar a shafinta na intanet.

Ishaq Akintola
2023: MURIC Ta Ragargaji INEC Kan Yin Taron Siyasa A Cikin Coci. Hoto: @thecableng.
Asali: UGC

Abin zargi ne INEC ta dauki taron siyasa ta kai shi coci - Akintola

A cewarsa, hedkwatar INEC da ke Legas ta shirya taro a ranar Alhamis kuma masu shirya taron sun zabi cocin Archbishop Vining Memorial Church Cathedral, Ikeja don yin taron kuma kwamishinan INEC, Mr Olusegun Agbaje zai halarci taron.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Wani sashi na jawabinsa:

"Wannan abin takaici ne. Ta yaya hukumar zabe kamar INEC za ta zabi wurin ibada a matsayin wurin taro? Shin taron na kiristoci da ke INEC ne ko mene? INEC za ta gaba da mambobin coci ne? Ba za a amince ba.
"Hedkwatar INEC ta Legas ta dau mataki na bogi. Yin taron hukumar zabe a coci kamar yin taro ne a sakatariyar jam'iyyar siyasa. Zai janyo waswasi. Bai dace ba musamman yadda coci ta nuna a fili cewa tana da ra'ayi a harkokin zaben da ke tafiya.

Akintola ya yi kira da shugaban INEC na kasa ya gargadi INEC ta Legas

"Me yasa za a zabi coci duk da daruruwan wuraren taro a Legas? Shin INEC tana dabbaka bukatun coci ne a zaben 2023? Wannan hadin baki ne? Dole hedkwatar INEC a Legas ta nuna wa yan Legas cewa za a kirga kuri'unsu. Muna kira ga yan Legas sun sanya ido kan INEC daga yanzu don ba mu gamsu ba ta nuna bangaranci ba."

A cikin sanarwar, ya shawarci INEC ta dena yin amfani da coci ko wani wurin ibada don yin taro sai dai idan taron dama don mabiya addinin aka shirya.

Ya ce INEC ba ta da wani alaka da wuraren ibada don yin tarurukanta yana fatan hedkwatar INEC na kasa da ke Abuja za ta gargadi hedkwatan Legas.

MURIC ta bukaci a dauke cibiyoyin WAEC, JAMB daga cocin RCCG

Kungiyar MURIC ta bukaci hukumar shirya jarrabawa ta JAMB da WAEC su dauke cibiyoyinsu daga cocin RCCG da ke hanyar Legas zuwa Ibadan.

Farfesa Akintola, shugaban MURIC, cikin sanarwar da ya fitar ya zargi cocin na RCCG da hana dalibai musulmai shiga harabarta don gudanar da hidindimun jarraba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel