Hadimin Buhari Ya Bayyana Asarar Naira Tiriliyan 10 da ke Jiran Najeriya a 2023

Hadimin Buhari Ya Bayyana Asarar Naira Tiriliyan 10 da ke Jiran Najeriya a 2023

  • Tsagerun da suke fasa bututu, suna sace danyen man fetur za su jawo ayi asarar Dala biliyan 23 a shekarar 2023
  • Janar Babagana Monguno ya nuna wannan zai iya yin sanadiyyar da N10.2tr za su ki shiga cikin asusun tarayya
  • Babagana Monguno ya kafa kwamiti da za suyi bincike a kan satar arzikin kasar, sai a mikawa gwamnati rahoto

Abuja - Mai ba shugaban kasa shawara a kan harkokin tsaro, Manjo Janar Babagana Monguno ya yi hasashen asarar makudan kudi a shekarar 2023.

An rahoto Manjo Janar Babagana Monguno mai ritaya a gidan talabijin na Channels TV yana cewa gwamnatin tarayya za ta iya yin asarar Dala $23bn.

Mai ba shugaba Muhammadu Buhari yake cewa za a rasa wadannan kudi ne a dalilin satar danyen mai.

Kara karanta wannan

Aisha Buhari: Da Gaske Aminu Ya Gana Da Shugaban Kasa? Gaskiya Ta Bayyana

Hadimin shugaban kasar ya gabatar da jawabi a wajen kaddamar da wani kwamiti na musamman da aka kafa domin duba matsalar satar danyen mai.

Ganga miliyan daya ake samu

Janar Monguno ya nuna damuwarsa cewa ganga miliyan daya Najeriya take hakowa a rana, a maimakon gangunan danyen mai biyu da OPEC ta ware.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar Monguno, kudin da ake samu daga bangaren fetur ya yi kasa, don haka ya yi kira ga ‘yan kwamitin da aka rantsar su magance matsalar kasar.

Babagana Monguno
NSA Janar Babagana Monguno Hoto: barristerng.com
Asali: UGC

Kwamiti zai yi aiki zuwa Fubrairu

Zuwa karshen watan Fubrairun 2023, kwamitin zai gabatar da rahoton binciken da ya yi. Rahoton nan ya fito a jaridar The Cable ta ranar Talatar nan.

Idan ba a samu dabarun da za ayi amfani da su wajen tsaida ta’adin da ake yi a yankin Neja-Delta ba, Naira Tiriliyan 10 ba za su shiga baitul-mali ba.

Kara karanta wannan

Lauya Ya Fadi Dalili 1 da ya sa ‘Yan Sanda Janye Karar Mai 'Cin Mutuncin' Aisha Buhari

Hakan na zuwa ne a lokacin da Najeriya take kukan rashin kudin shiga alhali gangar danyen mai tayi tsada a Duniya a dalilin yakin Rasha da Ukraine.

Kwanakin baya aka ji kamfanin NNPC yana cewa ya hada-kai da jami’an tsaro wajen ganin tsageru sun daina fasa bututun kasa, ana sace arzikin Najeriya.

Amma duk da haka, ana zargin cewa da kamfanin man da jami’an tsaro da wasu ‘yan siyasa ake hada-kai wajen yin wannan danyen aiki da ya dade.

Goodluck Jonathan: Abin da ya sa ake yin sata

A ra’ayin Dr. Goodluck Jonathan, an tsara dokokin Najeriya ne tun farko ta yadda ma’aikaci zai yi tunanin ya tanadi dukiyar haramun saboda gobensa.

An samu labari cewa Jonathan wanda ya yi mulki tsakanin 2010 da 2015 yace ba a ba ma’aikata damar kasuwanci, sannan idan sun yi ritaya ba a kula da su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel