Duniya Gidan Kashe Ahu: Bidiyon Yadda Jinjira Yar Kwana Daya Ta Yi Murtuk Da Fuska Ya Baiwa Mutane Mamaki

Duniya Gidan Kashe Ahu: Bidiyon Yadda Jinjira Yar Kwana Daya Ta Yi Murtuk Da Fuska Ya Baiwa Mutane Mamaki

  • Wata mai jego ta haddasa cece-kuce a soshiyal midiya bayan ta wallafa yanayin yadda jinjirarta ta yi da fuska awanni bayan haihuwarta
  • Mutanen da suka ga bidiyon jinjirar sun ce da alamna yarinyar bata shirya fadowa duniya ba tukuna
  • Mahaifiyar ta bayyana a sashin sharhi cewa jinjirar mace ce, don haka mutane basu shiga rudu game da jinsin yarinyar ba

Wata sabuwar uwa mai suna @kaylisticc, ta wallafa wani bidiyo na jinjira yar kwana daya da ta haifa da kuma yanayin yadda ta yi da fuskarta yayin da ta daga ta sama.

A cikin bidiyon, yarinyar ta yi kicin-kicin da fuskarta kamar dai wacce ta gaji da yanayin lamura.

Jinjira
Duniya Gidan Kashe Ahu: Bidiyon Yadda Jinjira Yar Kwana Daya Ta Yi Murtuk Da Fuska Ya Baiwa Mutane Mamaki Hoto: TikTok/@kaylisticc
Asali: UGC

Yayayin yadda yarinyar tayi da fuska ya haifar da martani

Yanayin yadda ta murtuke fuska ya baiwa mahaifiyarta dariya. Mutane da dama da suka yi kokarin fassara yanayin fuskarta sun ce yarinyar ta gaji tun ba'a je ko'ina ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Cike da barkwanci, wasu sun kara da cewar yarinyar bata shirya zuwa duniya ba tukuna, don haka take mamakin me take yi a nan.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

nessa ta ce:

"Wa ya ce maku ku fito dani waje."

Saabirah’s Garden ta ce:

"Duk bata yarda da ku ba tukuna, ina taya ki murna."

Deidra Davis yan ce:

"Duniya mai rudu....Yadda kike ji haka nima nake ji yarinya."

omodano ta ce:

"Babu abun da za ku ce mani, wannan kaka ce ta dawo."

McCall Joshua ya ce:

"Wannan hujja ne na cewa zuwa na daban suke yi a zamanin nan."

mcbudavz ya ce:

"Minti 2 a duniya nan har ta gaji da ita."

Ango ya yi murtuk da fuska yayin da amarya ke kwasar rawa a liyafar bikinsu

A wani labari na daban, wani ango ya haddasa cece-kuce a shafukan soshiyal midiya bayan ya daure fuskarsa tamau yayin da yake kallon amaryarsa tana kwasar rawa a wajen liyafar bikin aurensu.

An dai gano ango tsaye kikam yayin da mahalarta bikin suka yayyame su cikin farin ciki. Wannan ya sa mutane dasa ayar tambaya kan ko dai auren dole aka yi masa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel